•••MATAR AURE••• NAYI SOYAYYA DA MATAR - TopicsExpress



          

•••MATAR AURE••• NAYI SOYAYYA DA MATAR AURE..... Tabbas ba ko wace dariya bace farin ciki ke kawowa ba, haka kuma bai zama dole ba ace duk sandda kaga mutum yana murmushi kayi tunanin alkhairi ne acikin zuciyarsa. A wasu yan lokuta marasa tsawo da suka shude bana samun damar hawa sashin yanar gizo sai idan dare yayi. Wannan kuwa yana da nasaba da irin yanda lokaci yayi mani karanci. In har zan baku wannan labari dole ne na tuno da wani dare na jumaa wanda ya zamo shine silar baku wannan labari. Kodayake tun jiya nasha samun sakunni ta boye akan cewa mai zai hana nabar abin acikin zuciyata? Wasu kuma suna fadin intafi koto ayi mani bulala kawai, toh abinda masu wannan magana basu gane ba shi ne, Ai har gara ayi mani bulalar da in sake ganin irin ranar da asirin lamarin ya faru. Kamar yanda na saba ko wace rana ta Allah idan na dawo daga kasuwa nakan shiga bangaren yayana domin sanar dashi cewa na dawo daga kasuwa, koda kuwa na iske ya kulle. Koda ya ke ba wani dare nake yi ba sosai, sai dai nakan dauki lokaci ban iso gidaba saboda halin cinkoson jamaa da ke cikin birnin Abuja. A wannan rana agajiye na dawo,ga kuma fama da zazzafan tunani gami da kubucewar tunani na wanda suka samo asali sakamakon wata cinikayya da wata kyakkyawa tayi mani. A harkar kasuwanci na ba kasafai nake son shiga shirgin yanmata ba, sai dai duk sanda suka shigo nakan saki fiskata nayi wasa da dariya da su kamar dai yanda dokar cinikaiya ta ke. Ita ce macce ta karshe wadda na rufe cinki da ita. Kayan mata ne nake sayarwa na zamani, duk wasu abubuwa na kyale kyale ina sayar da su. Zaka iya hada kayan lefe ko kuma kayan daki duk irin wanda kake bukata tamkar akasar Dubai. A sanda ta shigo ina cikin kokarin rufe tankamemen shagonne,amma ganin yanda naga tana ta sauri yasa na dakata. Shigowarta keda wuya sai ta wuce kai tsaye inda na ke ajiye kayan bacci, wannan ya tabbatar mani da cewar ba shi ne karo na farko da ta fara shigowa shagonba. Akwai sabbin fitowa na zamani wanda na siyo wannan karon daga kasar (china). Ana kiransu da suna(sweetness Bby), bakwa bukatar fassara,dan haka zanci gaba da labarina kai tsaye. Kayan suna da tsada kwarai, domin tunda na kawo su ba kowa ne ke sayensuba. Kala biyu ta dakko, da yake kidinsu na manne ajiki bansha wahala gurin ciniki da ita ba. Bayan da bani kudin sai kuma ta bukaci na bata lambata domin suna da wata sayyar aure da zasuyi nan bada jimawa ba. Jin hakan yasa nace mata toh ko dai ke ce amaryar murmushi tayi har sai da bakinta ya bude na hangi wani dan hakorin makka yana makale ajikin fararen hakoranta. Wannan magana da nayi mata na lura zancen yayi mata dadi, hakan yasa ta bude yarjakarta ta dakko cingam ta saka abaki. Sa kayi da gaske zakagane tana motsa bakinta, dan kuwa zan iya cewa ma kila hadiyewa ta ke yi. Wayata tana ajiye akan doguwar kantar da ke stakanina da farfajiyar shagon. Ita ma wayar sabuwa ce. Na siyota ne a (china) ban ankaraba sai naga wayar a hannunta tana dibawa. Kai tsaye ta ce da ni agaskiya wayar nan ta bani shaawa, ina ka siyota? Kai tsaye nima na bata amsa da cewar kasar (china). To adaidai lokacin ina kan (fxbk) ne, hakanne ya bata damar tambayata sunan da nake amfani da shi domin muci gaba da magana ta ko wacce fiska. Ban boye mata ba komi ba, dan haka sai na fada mata. Haka dai muka rabu akan cewar zanga sako bayan na koma gida. Da isata gida sai na wuce dakina kwai. Yau banma je gurin yayana ba,da shigata daki sai na fada kan katifa zuciyata nata faman kulla biyar da goma akan wannan baiwar Allah. Bayan nayi alwala nayi sallah sai nayi kwanciyata kawai. Runtse idanuna nayi,amma ita nake gani. Kada mai karatu ya dauka cewar wai ko sonta nake, kawai dai ina tunanin duk irin zancen da mukayi da ita ne. Toh idan ma sonta nake nasan ta cancanci hakan. Ina cikin wannan yanayi ne sai bacci ya kwashe ni, baccin nawa yayi nisa kwarai, domin naga abubuwan zolaya acikin sa masu yawa. Daga ciki har mafarki nayi wai duk wata macce budurwa wadda take shiga yanar gizo wai na aureta. A kwai wata yarmage da nake kiyo, ita ce ta hau saman jikina wanda hakan yasa na farka daga baccin da nake yi mai hade da zolaya. Ni kaina sai da na kece da dariya. Toh in banda abuna ina zan kai wadannan yanmatan? Wannan ai sai dai irinsu (Hannu na mai kafada)hahhahahaha*ba kama suna* a gefena akwai ruwa da na ajiye acikin roba, da shi na taho tun daga kasuwa, sanyinsa yayi mani yawa shiyasa banshaba. Amma tuni naji yayi dumi, hakan yasa na gane cewar lallai na jima ina wannnan baccin mara amfani. Na dakko ruwan na dan watsa afiskata sannan na jowo wayata. Na daga kai na kalli agogon bango naga karfe biyu da rabi daidai na dare. Yanar gizo na shiga, da budewata naga anturo mani sakon neman izinin zama aboki. Na duba sunan da kuma hoton mai sunan. Kyakkyawar da tayi sayayya gurina ce dazu na gani. Ga kuma hoto ta turo mani ta akwatin sakona. Hoton sanye take da kayan baccin da ta saya agurina. Ga abinda tace mani daga kasan Hoton............. Zanci gaba..... {Mk}
Posted on: Mon, 28 Oct 2013 00:14:31 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015