ME MUSLMI YA KAMATA YAYI IDAN YAGA RUBUTUN DAN SHI,AH AKAN FALALAR - TopicsExpress



          

ME MUSLMI YA KAMATA YAYI IDAN YAGA RUBUTUN DAN SHI,AH AKAN FALALAR SAYYIDINA ALIYYU R.A Hakika kowane musulmi nagari Zuciyarsa cike take da kauna da nuna Soyayya ga Sayyidina Aliyyu R:A. Da Nana Fatimah, da Alhasan da Alhusaini da sauran Iyalan Annabi s.a.w masu tsarki, masu albarka Allah ya aminta dasu. Kamar yadda kuma Zuciyarsa ke cike da kauna da Soyayya da girmamawa ga duk sauran Sahabbai baki dayansu ba tareda ware ko daya ba. Hakika mai wannan siffa shine cikakken Musulmi mai Imani da Alkhairi atare dashi. Sau da yawa zamu na ganin rubuce-rubuce afacebook ko agidajen radio wadda ma,abota mummunar akidar nan ta SHI,AH ke gabatarwa wajen ambaton falalar Aliyyu r.a ko wani daga Ahlul baiti, to abinda ya kamaceka kai Musulmi wadda kayi Imani da Allah da Manzonsa Imani na hakika, ka kuma aminta da dukkanin Sahabbai ba tareda wariya ba shine ka kauda kanka daga wadannan Falaloli da Yan Shi,ah ke ambata, dalili kuwa shine: kashi 90 acikin 100 na abinda suke ambata KARYA ce! SHACI FADI ne! Wasu ne kawai suka Zauna suka kirkiresu domin son ransu da kuma goyon bayan akidarsu. Hakika kai amatsayinka na Musulmi mai addini da kuma karatu ya isarmaka Ingantattun Falaloli na wadannan bayin Allah da suka Inganta cikin littafan hadisai na Musulunci da suka tabbata irinsu Sahihul Bukhariy, Muslim, da sauran abinda ya Inganta awasu littafan na daban. Amma mafi yawan abinda ke zuwa alittafan Shi,ah na falalar Ahlul baiti Karya ce wadda bata da Asali balle makama. Wai kuwa shin kanada sanin cewa Shi,ah basu fara rubutun hadisai ba sai da Ahlussunnah suka fara da sama da shekaru 300 da wani abu??? Wannan yasa duk wata Falala Ingantacciya da ta Inganta daga Manzon Allah s.a.w akan Falalar Aliyyu r.a, ko wani daga Ahlul baiti to Ahlussunnah ne suka fara ambatonta, su suka fitowa da al,ummah ita! Ba dominsu ba to da Shi,ah basu santa ba ma! Shin kanada sanin cewa SHI,AH basu da riwaya ko guda daya 1 rak wadda take ta karan kansu ce INGANTACCIYA wadda tazo alittafansu??? Indai kaga riwayar hadisi Ingantacce alittafin Shi,ah to asalinta daga Ahlussunnah take idan ka koma littafan Sunnah zaka sameta. Hakika Shi,ah fa ba addini ba ce tarkace ne da Shirme da Fagamniya. Ya kamata kowa ya fadaka da wannan. Ahlussunnah su suka san darajar duk wani mai daraja, su kuma ke bayyanata yadda ya kamata. Allah yasa mu fahimta.
Posted on: Fri, 25 Oct 2013 14:33:23 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015