ME YA FARU A KARBALA 2 Assalamu alaikum jamaa. Ina kara jaddada - TopicsExpress



          

ME YA FARU A KARBALA 2 Assalamu alaikum jamaa. Ina kara jaddada barka da sallah a gare ku gaba daya. Allah ya karbi ibadarmu. Zamu ci gaba da darasi na biyu a yau in sha Allah. Tun da farko zai yi kyau mu soma da takaitaccen tarihin mutane biyu wadanda zancen Karbala yake kewaya a kan su. Su ne: Sayyidina HUSAINI bin Ali da kuma YAZIDU dan Sayyidina Muawiyah. Wane ne HUSAINI? Shi ne jikan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam HUSAINI Dan Ali Dan Abu Dalib Dan Abdulmuttalibi Dan Hashimu Al Hashimi. Mahaifiyarsa ita ce Fatimah Diyar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam. An haife shi a cikin watan Shaaban na shekara ta hudu bayan hijira. (watanni 11 ke tsakanin sa da wansa Al Hasan). Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam ne ya sanya masa suna, ya kuma yanka masa rago. A Lokacin wafatin Manzon Allah Sallalahu Alaihi Wasallam HUSAINI na da shekara 6 da wata 7. HUSAINI ya fi kowa kama da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam ta kasan jikinsa. Amma Al Hasan ya fi shi kama da shi ta saman jiki. Sun tashi kamar tagwaye saboda kusancin shekarunsu kuma Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam ya kasance yana son su da kaunar su irin so da kaunar da ba sa boyuwa. Ya kan kuma yi musu addua yana cewa, Ya Allah! Hakika ina son su, Ya Allah kai ma ka so su. Wannan ya sa masu kwarjini da kauna ba na wasa ba a wurin Sahabbai wadanda kaunar da suke ma Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam ta sa suna son duk abinda yake so kuma yake kauna. HUSAINI ya yi tarayya da Dan uwansa Al Hasan a wata falala wadda suka kebanta da ita, ita ce kasancewar su shugabannin matasan aljanna. (Al Jami na Tirmidhi, Hadisi na 3768 da Al Musnad na Ahmad (3/3 da 3/62) da Al Mustadrak na Hakim (3/167). Kuma Tirmidhi ya inganta shi. Via Dr Mansur sokoto ~Muhammad Ibrahim Bawa~
Posted on: Wed, 16 Oct 2013 07:26:38 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015