ME YA FARU A KARBALA 23 Wa ya kashe sayyidina HUSAINI? Bayan duk - TopicsExpress



          

ME YA FARU A KARBALA 23 Wa ya kashe sayyidina HUSAINI? Bayan duk bayanin da ya gabata na abinda ya faru, muna son amsa wannan tambaya. WA YA KASHE SAYYIDINA HUSAINI? Amma a wannan karon littafan Shiah kadai muke son su bada amsa. 1. Ga abinda Allamah As Sayyid Muhsin Al Amin ya fada a cikin Ayanus Shiah (1/34): بايع الحسين عشرون ألفا من اهل العراق، غدروا به وخرجوا عليه وبيعته في أعناقهم وقتلوه Mutane 20,000 daga yan Iraqi sun yi ma Husaini mubayaa, sun YAUDARE shi kuma suka fito a kansa, alhali mubayaarsa na ga wuyansu, kuma suka kashe shi. 2. Ga kuma abinda Hurru bin Yazid - daya daga cikin yan rakiyar Husain -ya ce ma rundunar da take kokarin kashe HUSAINI a Karbala: أدعوتم هذا العبد الصالح، حتى اذا جاءكم اسلمتموه، ثم عدوتم عليه لتقتلوه، فصار كالاسير في أيديكم؟ لا سقاكم الله يوم الظمإ. Yanzu zaku kira wannan bawan Allah na kirki, sai da ya zo maku sannan ku mika shi, sannan ku yi tsalle a kansa don ku kashe shi, har ya zama kamar wani fursuna a hannunku?! Kada Allah ya shayar da ku ruwa a ranar kishirwa. Duba AL IRSHAD na Al Mufid, shafi na 234 da ILAMUL WARA BI ALAMIL HUDA na Tabrasi, shafi na 242. 3. Sai kuma abinda Tabrasi ya hikaito cewa shi kansa sayyidina Husaini (R.A) yana cewa: ألم تكتبوا إلي أن قد أينعت الثمار ، وإنما تقدم على جند مجندة؟ تباً لكم أيها الجماعة حين استصرختمونا والهين ، فشحذتم علينا سيفاً كان بأيدينا، وحششتم ناراً أضرمناها على عدوكم وعدونا، فأصبحتم ألباً على أوليائكم وسحقاً، ويداً على أعدائكم. استسرعتم إلى بيعتنا كطيرة الذباب، وتهافتم إلينا كتهافت الفراش ثم نقضتموها سفهاً ، بعداً لطواغيت هذه الأمة Wai kam ba ku ne kuka rubuto mana cewa, yayan itace sun nuna ba, kawai zamu zo mu sami hadaddiyar runduna? Allah ya abkar da halaka a gare ku ya ku wannan taron wofi! Tunda kun kwala mana kira a haukace, sannan kuka daga mana takobin da muke ganin a hannunmu yake (Zaku kashe mu da shi), Sannan kuka hura wutar da mun hasa ta ne don makiyanmu kuma makiyanku. A yanzu kun zama masu fada da masoyanku, masu hada kai da makiyanku. Kaico! A Lokacin da kuke bamu mubayaa kun yo sulu kamar fari amma a yanzu kun kakkabe hannayenku kamar ba ku ne ba. Kai, Allah dai ya nisantar da ku ya ku dawagitan wannan alumma Duba ILAMUL WARA na Tabarsi, shafi na 949. 4. A nan ne kuma - in ji Mufid - sayyidina Husaini ya yi masu bakar addua yana cewa: اللهم إن متعتهم إلى حين ففرقهم فرقاً واجعلهم طرائق قددا، ولا ترض الولاة عنهم أبدا، فإنهم دعونا لينصرونا، ثم عدوا علينا فقتلونا Ya Allah! In har ka tsawaita rayuwarsu to, ka tarwatsa su, ka hahhargitsa su, kada ka bari su ji dadin mai mulki ko wane ne sam. Hakika sun kira mu da sunan taimakon mu amma sai suka zabura a kan mu zasu kashe mu. Duba ALIRSHAD na Al Mufid, shafi na 241 da Kashful Gummah na Arbili (2/18 da kuma 2/38). 5. Al Yaqubi a cikin Tarihinsa (1/235) shi kuma cewa ya yi, Zainul Abidin dan sayyidina HUSAINI wanda Allah ya kaddari ya kubuta ba a kashe shi ba a Karbala shi ma ya jingina kisan Husaini da iyalansa ga yan Shiah, mutanen Kufa duk kuwa da kukan munafurci da ya tarar suna yi. Ga maganarsa nan da nassinta: لما دخل علي بن الحسين الكوفة رأى نساءها يبكين ويصرخن فقال: هؤلاء يبكين علينا فمن قتلنا؟. A lokacin da Ali bin Al Husain ya shiga Kufa - yana nufin bayan rikicin Karbala - sai ya tarar da matan garin na ta kuka da hargowa, sai ya ce, Af! Dubi wadannan wai mu suke wa kuka. To, wa ya kashe mu ne? Zamu takaita a haka, sannan mu garzaya birnin Sham wurin Yazidu mu ji abinda yake faruwa a can. Ku dakace mu. Via Dr Mansur Sokoto Muhammad Ibrahim Bawa
Posted on: Sun, 27 Oct 2013 09:38:14 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015