Manzon Allah (S.A,W) ya ce: “Ya ku mutane ku tuba ga Allah - TopicsExpress



          

Manzon Allah (S.A,W) ya ce: “Ya ku mutane ku tuba ga Allah ku nemi gafararsa haqiqa ni ina tuba a kowanne wuni sau dari” (Muslim). Sannan An karbo daga Abu Huraira (R.A) ya ce: “Na ji Manzon Allah (S.A.W) yana cewa: “Na rantse da Allah ina neman gafarar Allah da kuma tuba a gare shi a kowanne yini sama da sau saba’in. (Bukhari). WANDA BAI TABA YIN KUSKURE BA YANA TUBA FIYE DA SAU SABAIN A RANA. NI & KAI & KE Da muke sabawa Mahaliccin mu kullum sau nawa Muke Tuba ??? SHIN MUNA TUBA FIYE DA SAU 70 A RANA ?? WAJIBIN MU NE MU TUBA GA ALLAH kuma mu sani cewa ba yawan istighfari ne kawai tuba ba,Tuba yanada sharudda kamar haka: 1. Qauracewa aikata sabo nan take (acikin lokacin da ake aikatata). 2. Yin NADAMA (takaicin) abin da aka aikata (abun da ya gabata na Sa6o). 3. Yin niyya Baza a sake komawa kan wannan zunubinba har abada. MU YAWAITA YIN ISTIGHFARI Fadin→→→ ASTAGFIRULLAH Allah mun tuba gareka ka gafarta mana dukkan kura-kuren mu. ﺳﺒﺤﻨﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ ﺍﺷﻬﺪ ﺍﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺍﻧﺖ ﺍﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻪ Ameen Ya Allah.
Posted on: Wed, 06 Nov 2013 20:33:01 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015