Me yasa kuke kukan rasa ni? An bada labarin wani bawan Allah da - TopicsExpress



          

Me yasa kuke kukan rasa ni? An bada labarin wani bawan Allah da yake kan gargarar mutuwa, sai dangi suka kewaye shi suna kuka. Sai yace ku tashe ni zaune, sai suka zaunar da shi sai ya fuskance su ya dubi uban sa yace me yasa kake kukan rabuwa da ni? Yace ina jimamin rashin ka da yadda zan yi da kewar ka bayan ka rasu. Sai ya juya ga mahaifiyar sa yace umma me yasa kike kukan rasa ni? Tace saboda zan shiga kuncin rayuwar rasaka. Sai ya juya ga matar sa kefa me yasa ki kuka? Tace zan rasa dadin zaman da muka yi ga shi kuma ban san hannun wanda zan fada ba. Sai ya juya ga yayan sa kufa me yasa ku kuka? Suka ce saboda zamu zama marayu bamu san irin wahalar da zamu shiga ba bayan baka nan. Daga nan sai ya dube su ya fashe da kuka. Gaba daya suka dube shi kai kuma me yasa ka kuka? Yace naga kowa yana kukan rasa ni ne saboda bukatar kansa! Shin a cikin ku akwai wanda yake kuka saboda doguwar tafiyar dake gabana? Koko akwai wanda yake kuka saboda rashin isashshen guzuri na? Ko akwai wanda yai kuka don zaa turbuda ni a turbaya ko abin da zan tarar na mummunan hisabi? Ko ko akwai wanda yake kuka saboda tsayuwa ta a gaban rabbil izzati ban san me zan tarar ba? Daga nan sai yayanke jiki ya fadi, sai su kai kan sa suka juya shi sai suka ga ashe ya mutu. Waka * Ga doguwar tafiya gabana Amma guzuri na bai isana * Ga karfi na ya raunana kuma mutuwa tana bidana *Ga dai zunubi fiye da sanina Amma Allah ya san ciki da bayana Allah yasa mu cika da imani fta
Posted on: Tue, 19 Nov 2013 06:06:57 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015