Mu shaqata! Wani Dattijo ne yake mura, sai yazo wajen wani mai - TopicsExpress



          

Mu shaqata! Wani Dattijo ne yake mura, sai yazo wajen wani mai kanti neman ROBB, mai kanti yace babu. Dattijo yace to Mentholatum fa? Mai kanti yace babu, Dattijo yace Tiger fa? Mai kanti yace duk babu sai LOKO kuma shi zafi gare shi sosai Dattijo yace Kai yaro wani zafi? Mu da muke shaka TEAR GAS idan muna mura a lokacin da muke aikin soja a Yakin duniya na farko. Mai kanti ya dauko masa LOKO ya bashi. Nan take dattijo ya lakato ya tura a hancinsa, ya kara lakatowa ya tura a dayan. Kafin mai kanti ya kawo canji Dattijo ya fara tsalle saboda azabar da yake ji. Dattijo ya waiwayo kan me kanti yace kai yaro, duba mun ka gani akwai Hanci a fuskata kuwa? Mai kanti yace Eh mana baba, hancinka yana nan. Dattijo yace To amma feshin wuta yake ko?!
Posted on: Sun, 10 Nov 2013 15:31:47 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015