Muhd Sayyadi Jibia wrote: Wani saurayi ne yaje wajen uban - TopicsExpress



          

Muhd Sayyadi Jibia wrote: Wani saurayi ne yaje wajen uban budurwar sa, neman aure, yana shan taba; UBAN BUDURWA: Wannan wace irin rishin kunya ce, kazo mani kana shan taba. SAURAYI: Kayi hakuri, duk idan na sha giya ne, dole ce sai na sha taba. UBAN BUDURWA: Wato har giya ma kake sha! SAURAYI: Aa ba halina bane, idan naje gidan rawa ne, nike dan shan giyar da abokai. UBAN BUDURWA: Kai! Har gidan rawa ma kake zuwa? SAURAYI: Gaskia da ban zuwa, bayan fitowa tane daga gidan yari na fara zuwa. UBAN BUDURWA: Iyeh! Har gidan yari ma kaje ke nan? SAURAYI: Kaddara ce ta kai ni, don na kashe wani mutum. UBAN BUDURWA: Tap di jannan, wato kai har rai kake kashe wa, amma kazo neman auren ya ta. SAURAYI: ehh, na kashe baban wata budurwa ta ne da ya hana ni auren ta. UBAN BUDURWA: Maraba Maraba da zuwa, yaushe ka shirya ai maku auren.
Posted on: Tue, 12 Nov 2013 19:31:44 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015