NAJERIYA TA KAFA TARIHI A GASAR KARATUN ALQURANI TA DUNIYA! A - TopicsExpress



          

NAJERIYA TA KAFA TARIHI A GASAR KARATUN ALQURANI TA DUNIYA! A KARO NA FARKO DAN NAJERIYA YA ZO NA DAYA A MATAKIN HIZB SITTIN DA TAFSIR A GASAR KARATUN ALQURANI TA DUNIYA TA SARKI ABDULAZIZ DA AKE YI SHEKARA-SHEKARA A BIRNIN MAKKAH NA QASA MAI TSARKI. A ranar da aka rufe gasar karatun da kasashe a ko ina a fadin duniya ke halarta, KABIRU ABUBAKAR daga jahar Kano ne ya zo na daya (1st position) a matakin Hizb Sittin da Tafsir, kuma na farko da ya taba samun wannan matsayin daga Najeriya tun shigarta a jerin kasashen da ke halartar gasar. Daga bisani NAZIRU ABUBAKAR SULAIMAN daga jahar Sokoto wanda ya wakilci Najeriya a matakin Hizb Sittin (tilawa) ya zo na biyar (5th position). Sannan ABUBAKAR daga jahar Jigawa wanda shima ya wakilci kasar Najeriya a matakin Hizb Arbain ya zo na uku (3rd position). Muna taya wadannan zaratan matasa da suka daga darajar kasarmu Najeriya a cikin kasashen duniya murna da farin cikin samun matsayi. Muna fatar samun nasara a wasu shekaru masu zuwa, Amin.
Posted on: Mon, 02 Dec 2013 06:48:10 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015