NANA A,ISHA BABARMUMINAI CE!!! YAN SHI,AH KUN MAKARA, NANA - TopicsExpress



          

NANA A,ISHA BABARMUMINAI CE!!! YAN SHI,AH KUN MAKARA, NANA A,ISHA TA TSALLAKE DUNIYA DA LAHIRA. KARANTA KA AMFANA IN SHA ALLAHU. بسم الله الرحمن الرحيم WACECE NANA AI,SHA R.A??? Amsa: Ita ce Ummul Muminina wato Uwar Muminai, Aisha bint Abi Bakar, mahaifiyarta itace: Ummu Rumaana bint Aamir, Mijinta shine: Fiyayyen halitta, Farin jakada, Annabin Allah Muhammad Rasuulullah S.A.W. Manzon Allah s.a.w ya aureta kafin hijra da Shekaru 2. WASU DAGA DARAJOJIN NANA A,ISHA R.A. ****************** Nana A,isha tana da darajoji da Falaloli masu tarin yawa amma ga kadan daga ciki: (1) AUREN MANZON ALLAH S.A.W: hakika duk macenda ta auri Annabi S.a.w to tagama dacewa, ta gama samun falala, ta gama zama mai daraja, saboda Allah ba zai zabawa Annabinsa, mafi soyuwarsa cikin halittunsa, dan gatansa MACEN AURE ba hakika sai tagari, sai mai daraja, to wannan itace kololuwar daraja da Matan Annabi s.a.w suka samu wato kasancewa taredashi, kamar kuma yadda ya tabbata Matansa aduniya suna cikin matansa a Aljannah. (2) ILIMI: Nana A,isha SHAKUNDUM ce wajen Ilimi, saboda haka nema ta kasance cikin SAHABBAI GUDA 6 da sukafi yawan ruwaito hadisai daga Annabi S.a.w, haka nan Nana Aisha Likita ce masaniyar magunguna da cututtuka, Sahabbai sun kasance suna aika mata tambayoyi na Ilimi tana amsa musu. (3) ALQUR,ANI ya sauka mussaman domin wanke Nana Aisha R.A da kuma tsarkaketa da barrantarda ita da nuna girman laifin masu taba mutuncinta ko Zarginta da wasu munanan kalmomi, jeka duba SURATUN-NUUR tun daga Aya mai lamba 11 har zuwa 21, wasu sukace har26 sun saukane musamman domin Nana Aisha R.A, duba Tafsirin Ibn Kasir, hakika wannan kadai ya Ishi Nana A,isha R.A Girman daraja da Falala. (4) Nana A,isha itace wadda Manzon Allah s.a.w yafi matukar kauna cikin matansa baya ga Nana Khadija r.a, ya tabbata ahadisin da Imam Albukhariy ya ruwaito cewa an tambayi Manzon Allah s.a.w Wa kafiso acikin mutane??? Sai yace A,ISHA aka ce cikin maza fa? Yace MAHAIFINTA. (5) MANZON ALLAH S.A.W yayi wafati akan cinyar NANA AI,SHA R.A, adakinta, anan kuma aka binneshi, yawunta ya hadu da yawunsa Hakika wannan ban ambaci komai ba daga falalar Nana Aisha R.A, amma wani abun mamaki Mabiya mummunar akidar nan ta SHI,AH sai suna Zagin wannan baiwar Allah mai daraja da falala, masoyiya ga Annabi s.a.w, kai harma ta kai ta kawo MALAMAN SHI,AH SUNA KAFIRTA NANA A,ISHA R.A, SUNA CEWA yar wuta ce jeka duba: TAFSIRUSSAAFIY, ko littafin HAKKUL YAKEEN na Majlisiy, ko Littafin MADIINATUL MA,AJIZ, da sauran littafan Shi,ah masu yawa. To dan Allah ga tambaya?? Duk mai Son Manzon Allah s.a.w da gaske zai Zagi Matarsa Abar kaunarsa??? Nana A,isha UWA ce ga Muminai wato masu Imani kamar yadda aya mai lamba 6 cikin suratul Ahzaab tayi bayani, to anan kaga ya tabbata duk wanda ya aibanta Nana Aisha to ya fitarda kansa daga cikin Masu Imani, domin dan kirki bazai muzanta Uwarsa ba. Hakika wannan zai kara fito mana afili cewa Shi,ah ba hanya ce ta gari ba! Shi,ah hanya ce ta halaka, Shi,ah ruguza musulunci take, Shi,a bala,i ce! Shi,ah Masifa ce! Shi,ah haramun ce! Ya yan uwa muso Nana Aisha r.a, mu girmama ta, mu barranta daga duk mai aibanta ta, mu sanyawa yayan mu Mata suna A,ISHA! A,ISHA! A,ISHA! Ni Kam ina fata Allah ya azurtani da yin Aure, ya kuma azurtani da samun yarinya domin na sanya mata suna A,ISHA. NANA AISHA KIN DACE KIN RABAUTA, ALLAH YA TASHEMU TAREDA KE BAIWAR ALLAH MAI GIRMA.
Posted on: Tue, 05 Nov 2013 09:59:38 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015