NURUL ALBABI ///05 CAMFI A KAN RANAKU Daga cikin abubuwan - TopicsExpress



          

NURUL ALBABI ///05 CAMFI A KAN RANAKU Daga cikin abubuwan da suka zama ruwan dare na musiba a wannan kasa akwai fdinsu, da suke cewa : “Wannan rana ce mai kyau” ko “Wannan rana ce mummuna”. To wannan duka karya ce kuma bidi’a ce haramtacciya wacce ta saba wa Sunnar Annabi Muhammad (S.A.W) da Sunnar Annabawa, da Manzanni, tsira da amincin su tabbata a gare su. Kuma babu daya daga Malaman Musulunci magabata, Salihai da Tabi’ai da ya karbi wannan. Haka nan Imam Malik da Shafi’i da Abu Hanifa da Ahmad binu Hambali, da kuma mabiyansu magabata da ‘yan baya babu wanda ya yarda da wannan. Ita wanna karya dai an dauko ta ne daga littafan Yahudawa da Kirista wadanda suka sauya addininsu, suka jefar da tafarkin Annabawansu a bayan bayansu, suka bi son zukatansu, suka batar da mutane da yawa, kuma suka kauce ga barin tafarkin madaidaici. Wannan batu shi ne gaskiya. Kuma bai halatta ga wani ya yi koyi da Yahudawa da Kirista ba saboda su kafirai ne ga Ijma’i. Kuma wanda duk ya yi tantama dangane da kafircinsu to shi ma ya kafirta ga ijma’in Malamai. Kuma abin da suke dangantawa ga Ka’abul Ahabari cewa ya yi hukunci irin wannan, to wannan ba ya inganta. Sai fa idan ya zama kafin Musuluntarsa ne, lokacin da yake a kan addinin Ahalul Kitabi. Kuma bai halasta ga wani ya yi hukunci da abinda Yahudu da Nasara suka yi hukunci da shi, kafin Musuluntarsu. Kuma Ka’abul Ahabari bai yi hukunci da wannan ba, bayan Musuluntarsa tun asali. Wannan ita ce gaskiyar magana. Sun kuwa masu fadin cewa, lallai mun san kwanuka duka na Allah ne, kuma rana ba ta amfanarwa ba ta cutarwa, amma, mun samu iyayenmu suna aiki da su don haka mu ma muke aiki da su, to wannan kuskure ne babba, kuma bidi’a ce haramtacciya. Ya wajabta a kan masu irin wannan magana su tuba, su nemi gafara, domin sun yi koyi da maganganun kafirai; « Kuma idan aka ce masu : ku bi abin da Allah Ya saukar, sai su ce, a’a muna bin abin da muka iske iyayenmu a kansa ». Wannan bata ne babba. Abin mamaki! Yaya suke zabar wasu kwanuka a bar wasu? Dukkan abin da zai amfani mutum dai biye yake da ci da sha, domin da su ne ginin dan Adam yake tashi. To yaya babu wata rana da ba su ci, su sha, amma ba ya cutar da su? To don me wanin wannan zai cutar da su? Wannan wauta ce, da sakaci da jahilci da bata, kuma bidi’a ce harambatacciya. A takaice dai, wanda duk ya zama ya yi Imani da Allah da ranar lahira, to kada ya yi hukunci da wannan jahilci, kuma kada ya yi aiki da shi, domin babu wani abu dangane da wannan da ya zo a cikin Alkur’ani mai girma, ko Hadisi ingantacce, kai ko ma a cikin Hadisai mai rauni. Hakika dai wannan abu an dauko shi ne daga littafan Ahlul Kitabi, wadanda suka sauya (addininsu) suka canja shi. Wannan ita ce gaskiyar, wacce babu kokwanto a cikinta. Mu tara gaba insha’Allah, duk a cikin littafin Mujaddadi Sheikh Danfodiyo Allah Ya rahamshe shi, “NURUL ALBABI”.
Posted on: Sat, 17 Aug 2013 06:23:06 +0000

Trending Topics



wap Samsung
para todos aqueles que acreditavam no trabalho e também para os
impotence reasons for
Joann Garzarella HERE is what will really help you. Your assuming
Did you know that stocksph/all.php real time data is more accurate

Recently Viewed Topics




© 2015