Najeriya ta karyata zargin yan kasarta a - TopicsExpress



          

Najeriya ta karyata zargin yan kasarta a Saudiyya _________________________________________ Tun da farko hukumomin Saudiyyan sun bai wa bakin waadin sabunta takardunsu Mahukuntan Najeriya sun musanta zargin cewa, ba sa kula da yan kasar da suka sami kansu cikin halin kaka-nika-yi a wurin da suke tsare a Saudi Arabia. Yayin da Saudi Arabiyar ke cigaba da korar yan kasashen wajen da ba su da cikakkun takardun zama a kasar, ko kuma na aiki. A wata hira ta waya da wani dan Najeriya a Saudiyya yayi da BBC, ya ce kawo yanzu ba wani jamiin Najeriya da ya ziyarce su, ga shi kuma su na fama da yunwa da rashin lafiya. Jakadan Najeriyar a Jeddah, Alhaji Ahmed Umar, shi ne ya musanta zarge-zargen da cewa suna bakin kokarinsu na kaiwa ga mutanen illa dai suna da yawa ne. Abun tambaya a nana shin minene dalilan da yasa yan Najeriya ke barin kasar su ta haifuwa zuwa wadansu kasashe dukda yake gasarsu najeriya tana daya daga cikin manyan kasashe mafi arziki a Afirica dama duniya baki daya? To amsar wannan tambaya itace kamar yada kowa yarigaya yasani cewa wannan kasa tamu najeriya babu Azalumar kasa mai cutarda al-ummarta irinta domin a duniya baki daya bau kasa guda wace takeda arziki irin na najeria wace yan kasar suke fuskantar rashin abinci, rashin tsaro, rashin ayyukkanyi ga matasa, rashin issashen ilimi, rashin ingatattun hanyoyi, rashin wutar lantarki, rashin imani da tausayin talakawa to lailai ya tabbata a Najeriya. Wannan shine babbar matsalar kasata najeriya domin rashin sghugabanci na adalci shine yajawo mana balaoin damuke ciki a kasarmu najeriya Shin wai ina mafita ?? By> Comrade Gusau
Posted on: Wed, 20 Nov 2013 16:45:23 +0000

Trending Topics



div>

Recently Viewed Topics




© 2015