O Tsuntsu MU SHA DARIYA Akwai wani mai arziki,yana da matarsa - TopicsExpress



          

O Tsuntsu MU SHA DARIYA Akwai wani mai arziki,yana da matarsa daya,da dansa daya (junior),da yar aiki (budurwa kyakkyawa),da kuma house boy.Suna zaune cikin jin dadi,komai a wadace. Wata rana maigida ya kawo giyarsa mai tsada ya ajiye a firji,ya fita da niyyar in ya dawo da daddare yaci abinci ya sha abarsa yayi tatul,kwatsam sai ga house boy,ya bude firji yana so ya sha ruwa,sai yayi ido hudu da giyar oga,to dama shima dan giyar ne, kawai ya kwashi giya ya koshi,sai ya cika kwalbar da yoghurt. Dare yayi oga ya zauna zai ci abinci,tare da uwar gida,shi kuma house boy yana kitchen yana ta tunanin me zai yi ya fidda kansa daga bacin ran oga.Nan dai oga yace uwargida ta dauko mai giyarsa,aka duba giya ta zama yoghurt,sai oga ya kwala wa house boy kira a fusace,yace,Bul us!!!, house boy ya amsa,oga yace,wanene ya shanye min giya ta,dama ya san halin Bulus,sai house boy yayi shiru, sai oga yace aah,sai ya tashi yaje kitchen ya same shi, yace, nayi kiranka ka amsa,amma na tambayeka baka bani amsa ba, sai house boy yace, ai oga wannan kitchen din ne in dai kana ciki to baza ka iya amsa ko wace tambaya ba,sai dai kawai ka amsa kira.Nan da nan ran oga ya kara baci,ganin cewa house boy ya raina mai hankali.Sai oga yace to tunda haka ne,ni zan tsaya a kitchen,kai kuma kaje waje ka tambaye ni,ko zan iya bada amsa? aka kirawo maman junior domin tayi shaida. House boy ya yarda,ya fito daga kitchen,domin yiwa oga tambaya,sai uwar gida tace,Bulus yi tambayar ka!!.Sai Bulus ya kwala wa oga kira,oga ya amsa,sai Bulus yace,wanene yake shiga dakin yar aiki idan madam bata nan??..sai oga yayi shiru,nan da nan ran uwar gida ya baci dan kishi,sai ta sake maimaita tambayar da karfi, amma inaaa, oga ba amsa. Sai Madam da Bulus suka koma kitchen,Madam ta tambayi oga cikin fushi,sai oga yace ai shima dai yana tunanin akwai wani abu a kitchen din nan,dan baiji komai ba banda kira, Madam ta nuna bata yarda ba,sai Bulus yace, to kema ki tsaya a kitchen,ayi miki tambaya ko zaki iya amsawa.Cikin fushi da karfin gwiwa,tace,jeka kayi zan amsa, ai oga munafiki ne,sai ta tsaya,su kuma suka fita,oga yana gefe,hankalinsa a tashe,sai Bulus ya kwalawa Madam kira,Madam ta amsa,sai Bulus yace,wanene baban junior na gaskiya!!! Madam tayi shiru,oga ya zabura cikin fushi,ya sake maimaita tambayar da karfi,amma Madam ba amsa,oga yaje ya tambayi uwar gida,sai tace gaskiyane,ita in banda kiran da akayi mata bata ji komai ba,oga yace karya kike munafuka ce ke........hahah a!!! IDAN KAI NE/ KECE YA KENAN!!? by ahmad a baba
Posted on: Sun, 27 Oct 2013 18:49:53 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015