RANAR QUDUS Palasdinawa ke jaddada bukatarsu ta ganin an kawo - TopicsExpress



          

RANAR QUDUS Palasdinawa ke jaddada bukatarsu ta ganin an kawo karshen mamayar da Isra’ila ke yi masu. Ranar ta Qudus, wadda Yau juma’a, al’ummar Palasdinu da kuma na wasu kasashen duniya, ke gudanar da zanga- zangar ranar Qudus, wato ranar da marigayin jagoran juyin juya halin kasar Iran Ayatullahi Komeini, ya kirkiro jim kadan bayana samun nasarar juyin juya halin musulunci na kasar ta Iran a shekarar 1979. Ranar tana a matsayin ranar da al’ummar Palasdinu da kuma sauran kasashe na duniya ke amfani da ita domin nuna bukatar ganin an samar da kasar Palasdinu mai cikakken ‘yanci. A zirin Gaza da kuma kuma sauran yankuna na Palasdinu, kamar dai sauran kasashen na duniya, a kowace shekara ana gudanar da irin wannan zanga- zanga a kowce juma’ar karshen watan Ramadana. A birnin Tehran na kasar Iran inda wannan rana ta samo asali, ana gudanar da zanga-zangar ne a karkashin jagorancin shugaban kasar mai barin gado, Mahmud Ahmadinejad. Zanga-zangar ta bana dai ta zo ne a daidai lokacin ake hawa teburin tattaunawa tsakanin Palastinawa da kuma Isra’ila, shekaru uku bayan dakatar da tattaunawar, yayin da shi kuma shugaban Isra’ila Shimon Peres ke cika shekaru 90 a duniya.. #great_boy
Posted on: Fri, 02 Aug 2013 17:52:56 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015