RIKITA - RIKITA! Na doka wani uban tsaki ganin ana nema ahanani - TopicsExpress



          

RIKITA - RIKITA! Na doka wani uban tsaki ganin ana nema ahanani sakewa cikin dare irin wannan wanda yanzu kusan karfe daya da wani abin, tun inajin karar kururuwar wayar tawa kamar a mafarki hartakai gana farka kuma na tabbatar da cewa ba mafarkibane. Ina farkawa kuma kiran wayar yana katsewa dan haka bandamu ba sai nakamo bargona domin karayin nutso a daddan barcina. Banfi minti biyu ba da kwanciyar sai wayar tawa takuma daukar kururuwar neman dauki daga gareni, cikin hasala namika hannuna izuwa ga wayar domin dai jin waye wannan yake neman hanani sakat cikin dare. Lamba ce gwara - gwara ta bayyana akan screen din wayar, wanda hakan yana nufin bani da lambar kenan akan wayata, kuma banajin zan iya daga wayar da bansan lambar ba kuma cikin dare irin wannan, dan haka sai na mayar da wayar batare dana aikata komai ba. A karo na hudu kenan da kiran wayar yakuma shigowa, dan haka tuni na yanke shawarar amsa kiran wayar. Kusan 30s nadauka bance komai ba bayan danaga wayar, can ban auneba sai najiyo wata siririyar murya mai kama da busar sarewa tafara magana Hmmn dan Allah ko waneni yayi hakuri, zaiga nadameshi dayawa, wlh mistake aka samune, ba kai nayi niyar yiwa TRANSFER dinba, dan Allah kayi hakuri kadawomin da kudin kaji Tuni dan guntun barcin daya rage a kwayar idanuna yayi fatalwa ya tsere, TRANSFER TA KUDI! Cikin shakewar murya nace ma..la..ma ban fahimci abinda kike nufi ba, nifa barci nake tika kawai naji kiran wayarki, dan haka inajin dai kinyi kuskuren wajen kiran lambar ne, amma ba wanda yamin transfer ta kudi alayina, hasalima yau kusan sati na daya rabon da wayata taji kanshin kudi Inagama bata amsa sai na katse kiran nata sakamakon wani gajeran tunani danayi, KANA SHIRMENKA WATA KILA ALJANA CE TAKE SON TAYI WASA DA TUNANINKA Ina ajiye wayar kiran yana kuma shigowa, tuni nafara karkarwa sbd tunanin daya ziyarceni tuni yasakamin TSORO. malam wlh da gaske nake, lambarka itace wadda nayi kuskure nayiwa transfer din, dan Allah kaduba messages dinka zakagani Cikin tsoro - tsoro nace To dan haka cikin gaggawa natafi domin cika umarninta wato na nufi Inbox din wayar. Ina ganin 777 nasan cewa mai dadin muryar nan tafini gaskia, tabbas ni tayiwa transfer din cikin rashin sani, cikin sauri na latsa akan 777 domin naga adadin kudin data turo. #10,000 was Transferred To you from the 080xxxxxxxx on 18/10/2013 01:12am via share & sell. Your New Account balance is #10,000,65 Tuni na mike zaune daga kwanciyar danake, DUBU GOMA! Kai! Ni da nake maleji da 65kobo amma sai gashi DUBU GOMA sunshigo a abinda bai wuce awa daya ba! Tab! Lallai wannan mai tattausan muryar dole ta rikice haka. Kamar tasan nagama karantawa kawai sai ga kiranta yakuma shigowa, Malam kagani ko? Wlh mistake aka samu, MASOYINA zanturawa amatsayin GIFT na Birthday dinsa shine aka samu akasi MASOYI tabdijan! Cikin dakushewar murya nace ikon Allah kenan, kinga nima kuwa masoyinkine wlh, dan tunda naji muryarki naji kingamayimin kuma nima rana ita yau xaayi Birthday dina... Bansan sanda na takarkare na fesamata wannan uwar karya ba, kawai sai jiyota nayi tana ta kyalkyala dariya, amma akwaika da abin dariya malam, kawai dan kaga kudi sai kazama GIZO... Ni dai kadawomin dasu inyaso idan naka Birthday din yazo sai kaima Masoyiyarka ta baka Gift din Wato dai wannan baiwar Allahr sotake tamin TALEKO TA KOMA kenan, inaganin tsurar kudi har DUBU GOMA amma ace na mayar dasu wai wani xaa turawa da Gift dinsu. Duk dabarun da xanyiwa maabociyar dadin muryar akan tace nabar kudin nayi amma naga alama hakana baxai cimma ruwa ba. Tuni wata dabarar ta kuma xiyartata cikin gaggawa, dan nan da nan sai nace To shikenan bari nagwada dawomiki dasu, amma kinsan me? MTN suna bina bashi fa dayawa sbd nahau kan tsare - tsarensu dayawa irinsu Caller Tunez da Mtn Play da Mtn Games da irinsu Mtn Data da kuma Mtn Family & Friends Bansan cewa a karyar dana tafkoba harda ta rainin wayo ba sai danaji amon sautin dariyarta yaki tsayawa. hehehehe... Wato harda su Family & Friends? Su family manya, wato shima plan din kudi ake dauka haka tsababa? Tuni na kame nakasa motsi sbd ni kaina sai yanzu nakejin kunyar kaina da kaina sbd wannan uwar karya dana feso duk dandai na samu naci kyautar DUBU GOMA wadanda tuni sunsami MASAUKI awajena!!!
Posted on: Fri, 18 Oct 2013 09:18:34 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015