RIQO DA SUNNAH - TopicsExpress



          

RIQO DA SUNNAH HUTU ------------------------------ Bismillahir-Rahmanir-Rahim ------------------------------ Wallahi matuqar ka samu kanka cikin riqo da Sunnah kana koyi da Annabi (Mai tsira da Aminci) cikin dukkan mu‘amalolinka na yau da kullum, iyakacin iyawarka, sannan kana hanuwa da dukkan abinda ya haneka to, ka godewa Allah! Domin ka ku‘buta daga dukkan fitintinu. Ash-Sheikh Barbahari (Rahimahullah) yana cewa: “Duk wanda ya taqaita akan Sunnar Annabi (Mai tsira da Aminci), da abinda Sahabbai suke kai da abinda Al‘ummar Musulmi (Jama‘ah) suke akai to, ya tsira daga ma‘abota Bidi‘a (‘Ya Bidi‘a) dukkansu, gangar jikinsa ya huta, addininsa ya ku‘buta -Insha Allah-. [SHARHUS-SUNNAH: Shafi na 274]. Saboda haka! ‘yan‘uwa kar mu damu da tsangwamar masu tsangwama, cutarwar masu cutarwa, da dukkan wani sharrance-sharrance da Qarerayi da akeyi mana! Kawai mu dai ma‘auninmu “Kitabu da Sunnah“ amma ba ruwanmu da zargin mai zargi. ALLAH ya tabbatar da duga-duganmu akan tafarkin shi
Posted on: Tue, 20 Aug 2013 22:16:21 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015