Rahoto-An kama wasu mutane guda biyu da ake zargi da kissan gillar - TopicsExpress



          

Rahoto-An kama wasu mutane guda biyu da ake zargi da kissan gillar fiye da mutane 60 a kauyen kizara dake tsafe ta jihar zamfara. Mutanen dai da aka kama angurfanar dasu a gaban gwamnan jihar zamfara domin ya gansu da idonsa kuma ya tabbatar ma da jami,an tsaro cewa dasu kaisu garin gusau da ransu domin ganin an samu yimusu tambayoyi. Gwamnan dai yana cikin wani dan karamin jirgin sama a lokacin da yar,isa garin na kizara kuma ya samu rakkiyar kwamishinan yan,sanda Alh.akila usman gwari da daraktan tsaron na farin kaya da kuma Emir na tsafe. A wannan satin ne dai wasu yan,ta,adda fiye da dari bisa babura sukaafkawa mutanen kizara inda suka kashe mutane fiye da 60 cikinsu harda sarkin garin da kuma limamin garin tare da shugaban yan,bangar ta kizara, Sanin kowa ne dai matsalar rashin tsaro na cima mutanen wasu yankuna na jihar ta zamfara tuwo a kwarya inda ko a makonni 3 da suka wuce wasu barayin shanu sun kai hari a kauyen dumburum dake karamar hukumar mulki ta zurmi inda suka kashe fiye da mutane 20 wadanda akace dukkansu fulanine makiyaya shanu. yayin da al,umar yankin dansadau dake karamar hukumar mulki ta maru da birnin magaji suma suke fuskantar turjiya akai a kai ta ramuwar gayya saboda yawan fafatawar da yan,kungiyar nan ta sakai wato banga inda suke kashe barayi soka barayi su kashe su kuma subi dare ko asuba su kashe duk mazauna gari, Don haka muna kira ga hukumar tsaro da ta gaggauta kara baza jami,an tsaro a wadannan yankuna masu fama da tashin hankali kuma gwamnati ta kara matsa kaimi da yin gargadi ga yan,banga dasu kiyayi kisan barayi batare da sanin jami,an tsaro ba domin ganin an samu saukin wannan matsala.
Posted on: Sat, 22 Jun 2013 21:11:18 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015