SAKO DAGA IMAMU AHLISSUNNAH WAL JAMAA (Shaykh Abdulwahhab - TopicsExpress



          

SAKO DAGA IMAMU AHLISSUNNAH WAL JAMAA (Shaykh Abdulwahhab Abdullah). SHIN IDAN RANA TA YI KHUSUFI ME YA KAMATA MUSULMI YA AIKATA? Assalamu Alaikum Wa Rahmatullahi Wa Barakatuhum. Muna kira ga yan uwa musulmi cewa idan Allah ya sa rana ta yi KHUSUFI to muna sanar da yan uwa cewa mu musulmi muna da tsari wanda annabi SAW ya dora mu akai idan har irin wannan ta faru. Ana zuwa ne a gabatar da Sallah, a roki Allah afuwa, sharrin da yake ciki Allah ya kare mu, alkhairin da yake ciki kuma Allah tabbatar mana. Ba daidai bane wasu su je suyi ta kide-kide da raye-raye, wannan alada ce ta maguzawa bai kamata ace mun yi koyi da su a irin wannan ba. Mu roki Allah da kyawawan sunayensa domin samun Rahamarsa. SIFFAR YADDA AKE YIN SALLAR KHUSUF - Shaykh Jabir Sani Mai Hulla Hadissai sun zo da siffofi daban-daban kan sallar; mafi ingancinsu shi ne hadisin Aisha da Ibn Abbas da ke cikin Bukhari da Muslim: zaayi karatu mai tsawo a rakaah ta farko ( kamar Baqarah) sannan a yi rukui kamar tsawon karatun, a daukako daga rukui a koma karatun da bai kai tsawon na farko ba, a koma rukui kamar karatun, idan aka daukako aje sujuda 2 kamar karatun...sai ayi a rakaah ta biyu kamar yadda aka yi a Rakaa ta farko.
Posted on: Sun, 03 Nov 2013 07:54:24 +0000

Trending Topics



day-Christmas-Gift-Ideas-100-Solid-Wood-Grand-topic-384454101712704">Holiday Christmas Gift Ideas ++ 100% Solid Wood Grand
I got Western, and it nailed nailed my profession. Lisa

Recently Viewed Topics




© 2015