SAƘO DAGA AMINA MUHD. YA YAUDARENI YAYI MIN CIKI. Dan Allah - TopicsExpress



          

SAƘO DAGA AMINA MUHD. YA YAUDARENI YAYI MIN CIKI. Dan Allah Admin Aisha Umar ni ma ki daure ki sanya min wannan labarin nawa ko zan samu shawara daga Jamaa. Sunana Amina Muhd ni yar jahar KANO ce kuma shekaruna 21. A kwai wani saurayi da muke soyayya dashi yau sama da shekaru 5 muna tare dashi cikin nuna so da ƙaunar junan mu. Muna cikin haka kawai sai na ga watarana yazo wajen ya haɗe fuska na juyin duniyar nan ya faɗa min laifin dana masa, amma wallahi. Haka dai muka ƙare hirar ya koma ba wani abin farinciki daga wajena ko wajensa. Tun daga lokacin yake neman juya min baya, ni kuma sai haƙuri nake bashi idan wani lafi na masa amma yaƙi ya sauko. Ina cikin gida watarana da dare da misalin ƙarfe 08:00pm ya kirani a waya cikin sanyayyar murya Amina ina son mu yi wata magana dake mai muhimmanci ki sameni a ɗakina. Da jin haka na yi sauri na shirya dan amsa kira masoyina dana san yake fushi dani. Da zuwana na iske shi a ɗaki cikin faraa da sakin fuska ya taryeni na ji daɗin ganin masoya ya sauka daga fushin da yake dani. Muna cikin haka sai na ga ya ɗauko min lemon GWANGWANI na MALTINA ya zuba min a cup ya bani, nan take na shanye duka muka dai cigaba da hirar mu, can wajen minti 3 zuwa biyar na fara jin kasala sai nan take kawai naji wani matsanin barci ya zo min. Sai jin nayi kawai na yi baya akan katifa na kwanta. Inna lillahi wainnailaihi rajiun! Allah ka saka min. Wallahi ban yafe masa ba dan ya cutar min da rayuwata. Ashe maganin barci ya zuba min a lemon dana sha, koda ya ga na yi barci ya shiga aikata mugun nufin sa akaina. Duk ina cikin magagin barci ba zan iya tuna komai ba. Da ya ƙare biyan buƙatar sa ya barni nan sai da ƙwayoyin maganin suka sake. Da farkawa ta na ga halin da nake ciki sai ƙwaƙwalwata ta kama tunatar dani abubuwan da suka faru. Na sha kuka na yi nadama na yi dana sanin haɗuwata da masoyin nawa. Daga ƙarshe na gyara jikina na kama hanya zuwa gida tun daga ranar kum mutumin nan ya daina kirana a waya idan na kira number shi a kashe ya can za SIM CARD. Bayan yan watanni da faruwar hakan sai na ga wani watan da yazo ban ga aladata ba, hankalina ƴa tashi nan take hankalina ya tashi na tabbata ba makawa ina da ciki sakamakon abin da ya faru dani sai dai cikin bai girma ba. Yanzu 0 ku taimakamin da shawarwari dan Allah. Da nayi tunanin na je da ƙawata wajen likita mu roƙe shi ya zubar min da cikin nan. Sai kuma ina saman fcbk a jiya na ga wannan dandalin. Ku taimakamin dan Allah da shawara ya zanyi? Wadda Ta Gabatar Admin Aisha Umar.
Posted on: Tue, 29 Oct 2013 12:19:50 +0000

Trending Topics



>
Some people are like seed along the path, where the word is sown.
Mmegi NewsWhy they were punished Why they were punished As the
Yesterday I spent a good deal of time at Cathedral Park and then

Recently Viewed Topics




© 2015