SHAIKH MUHAMMAD SANI YAHYA JINGIR (Shugaban Majlisar Malamai Na - TopicsExpress



          

SHAIKH MUHAMMAD SANI YAHYA JINGIR (Shugaban Majlisar Malamai Na Qasa JIBWIS NHQ JOS). Yace Sheikh Kabiru Gombe yana cikin yara Matasa, ban taba jin waazin sa ba kafin a hadu, ban taba ji ba, sau daya wallahi ban taba ji ba. Mun hadu da shi ranar da na yi kira (hadewa). Da yake Malam Kabiru Muzakkari ne (mai kokari). Yaku matasaaa ban da kwanciya. In aka kira Malam Kabiru ya yi waazi sai ka ji an yi kabbara, don menene? an san shi; akan me, a waazi, wanda yake yi a ina? A kwance (sai jamaa suka ce aa) ya tsaya ne ya yi (jamaa suka ce eh) . Bayan hadewa, da aka nuna min wani waazi da suka je suka yi a garin Ija Gwagi na jahar Niger, yan Darika ta Tijjaniyya da Rubabbun yan sanda da Rubabbun Masu Unguwanni suka sa yara na jifar su, ya zo ya kira Alaramma ya hau, ya ce wallahi kun makara, ya ce ina so inga jini na ya dige anan. Aiki ko kwanciya? (jamaa suka ce aiki) Jamaa mu mike mu duka da aiki Allah zai taimake mu duniya da lahira in Allah ya yarda To Maluma Matasa, kun ji Malam ya yabawa Sheikh Kabiru Gombe akan aikin da yake yi na waazi kuma yace mu tashi ban da kwanciya. Allah ya sakawa Shugaban Majalisar Malamai na Kasa Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir da Alkhairi, Amin. Lalle Sheikh Kabiru Gombe Haka Yake bayi da Tsoro akan Fadin gaskiya, Sai dai in ba a Fahimce shi ba, Allah ya bamu ladan ayyukan mu.
Posted on: Wed, 15 Jan 2014 16:50:07 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015