SHEIKH BAWA MAI SHINKAFA BAI KOYA MANA GABA BA. *TARIHI* lokacin - TopicsExpress



          

SHEIKH BAWA MAI SHINKAFA BAI KOYA MANA GABA BA. *TARIHI* lokacin da Izala ta rabu yan Jos suka dauki marigayi Sheikh Bawa Mai Shinkafa da gaba mai tsanani. Kullum basu da abin zagi sai shi, shi kuma bawan Allahn dayake bai riki kowa a zuciyar sa ba, lokacin daya ji labarin marigayi Sheikh Ibrahim Adam Mai Shafi baya da lafiya nan da nan ya gaggauta ya kai masa ziyara asibiti ya jajanta masa, sannan bayan ya koma gida duk dalibinsa daya zo gaishe shi sai ya umarceshi da yaje ya gaida Mai Shafi, su kuma dalibai duk wanda yaje sai ya gayawa mallam mai Shafi cewar ai mallam Mai Bawa Shinkafa ne ya turo su su duba lafiyar sa. Sheikh Ibrahim Adam Mai Shafi dai yana daga cikin jiga-jigan Sheikh Samaila Idriss a wancan lokaci. Lokacin da aka sallamo shi daga asibiti har kuka sai da yayi saboda yaga mutumin da suka sa a gaba da zagi da cin mutunci amma shi bai dauke su haka ba. Tun daga nan bai kara fadan wata mummunan magana game da Bawa mai shinkafa ba har Allah ya karbe ransa. Allah ya gafarta mar. Wannan labarin dana bayar tarihi ne yake maimaita kansa. Yanzu ka duba kaga yadda yan Jos suke daukan wasu malamai da gaba mai tsanani kullum suka bude bakinsu baka jin alhari sai dai suka ga wanda bai taba ko ambatosu ba. Misali yanzu in akace su kawo kasset guda daya tak wanda Bala lau ya aibata su wallahi-wallahi basu iya kawowa haka ma Jalo Jalingo, Alhasan Adam. Su dai kawai gabar ne shaidan ya cusa musu a zukatan su, dama haka rayuwa take. Wani lokacin sai kaga mutum ya tsane ka alhali kai baka masa komai ba. *TABARBAREWAR TARBIYA duk wanda yake Izala bangaren Kaduna ya ginu akan tarbiyya irin ta wancan labari dana baku na rashin daukan wanda kuka samu banbancin fahimta da shi a matsayin abokin gaba Daga karshe ina fatan yan Jos zasu daina gaba damu don mu ba abokan gabansu bane.
Posted on: Sat, 15 Feb 2014 21:24:05 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015