SHI,ANCI DAGA INA ZUWA INA??? RUBUTU NA (2). RUBUTAWAR ABU - TopicsExpress



          

SHI,ANCI DAGA INA ZUWA INA??? RUBUTU NA (2). RUBUTAWAR ABU ABDILHALIM MALAM NUHU UBALE IBRAHIM (HAFIZAHULLAHU). MA,ANAR SHI,AH AWAJEN MALAMAN MUSULUNCI. ****************** Idan Malaman Musulunci sukace: SHI,AH suna nufin wadanda suka Jibinci Ali dan Abi Talib R.A, da Iyalansa, kuma sukace shi WASIYYI ne na Manzon Allah S.A.A.W, kuma Nassi ne ya tabbatarda Khalifancinsa, sannan kuma suka Kafirta mafi yawancin Sahabbai R.A musammman ABUBAKAR da UMAR Allah ya yarda dasu. IMAMUZ ZABIDIY Allah ya jikansa yace: Wannan Suna na SHI,AH yayi rinjaye akan duk wanda ya jibinci Ali r.a da Iyalansa, kuma al,umma ce da ba zasu Kirgu ba wajen rarrabuwarsu, Fandararrunsu sune RAFILAWA masu limamai 12, suna Zagin Abubakar da Umar r.a, Kifaffun cikinsu kuwa suna kafirta Abubakar da Umar r.a, daga cikinsu akwai wanda ya kai matsayin Zindikanci duba TAJUL ARUS 5/144. Sharastaniy Allah ya jikansa yace: SHI,AH sune wadanda suka jibinci Ali r.a akebe, kuma suka ce Imamancinsa da Khalifancinsa Nassi ne ya nuna haka, kuma Wasiyya ce ta Annabi s.a.a.w ko dai aboye ko abayyane, kuma suka kudurce Imama ba zata fita daga yayansaba, in kuma ta fita to Zalunci ne daga waninsa ko kuma Takiyya ce daga gareshi duba ALMILALU WAN NIHAL 1/155. Ibnu Hazm Allah ya jikansa yace: Duk wanda yayi daidai da Shi,ah akan cewa Ali r.a shi yafi Falala acikin Mutane bayan Manzon Allah s.a.a.w kuma shine mafi cancanta da halifanci, sa,an nan Yayansa abayansa, to shi dan Shi,ah ne duba ALFISALU FIL MILALI WAL AHWA,I WANNIHAL 1/318. Abdullahi dan Ahmad dan Hanbal Allah ya jikansu, ya tambayi Mahaifinsa cewa: SU WANE NE RAFILAWA?? sai yace Masu Zagin Abubakar da Umar r.a duba Kitabussunnah na Abdullahi dan Ahmad dan Hanbal shafi na 343. Wannan shine ma,anar shi,ah awajen Maluman Musulunci, kuma wannan ma,ana irinta Malaman Shi,ah suka bata, kamar yadda zamuji arubutu na 3 In sha Allah. Dafatan Allah ya fahimtar damu gaskiya da ikon aiki da ita. Mu hadu arubutu na 3, na 1 da na 2 sun gabata.
Posted on: Mon, 25 Nov 2013 12:53:07 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015