SONSHI KUKEYI KO SON ABIN DA ZAI SHIGA ALJIHUNKU - TopicsExpress



          

SONSHI KUKEYI KO SON ABIN DA ZAI SHIGA ALJIHUNKU DAI............................... Allah sarki maigirma gwamnan jihar katsina Brr.Ibrahim Shehu Shema,a yayin da sauran jamaa suke maka taaziyyar rasuwar mahaifinka, mu anan garin kahutu akasin hakane yake faruwa,domin kuwa munanan aduoi ake dannawa akanka a masallatan jumaa da Islamiyyu da makarantun Allo, sakamakon dakatar da aikin hanyar da ta tashi daga DAbai zuwa Kahutu ta wuce Sundu wanda SANATA ABU IBRAHIM ya fara. Sai yabon yan jamiyar adawa akeyi ana shi masu albarka da yi masu adduoi da kwarai su da iyayensu. Amma abin banhaushi naka shike bada kai,sai ga yan PDP karamar hukumar Danja masamman yan PDP garin Kahutu sunki fitowa fili su sanar da kai gaskiyar abin dake faruwa kada furarsu ta bare. Kai harma barazana sukeyi da cewa duk wanda yayi rubutu ko yaje wani gidan Radio ya baiyana gaskiyar abin dake faruwa,idan maaikacine sai sunyi mashi sharrin da ka koreshi, idan kuma dan casual ne dama wannan a hannun su yake. Ya maigirma gwamna nasan kai mutum ne mai hankali mai ilmi mai tausayin talakawa INTERNATIONAL LAWYER kuma kwararren dan siyasa, baka aiki da jitata sai ka tabbatar. Maigirma gwamna aje agani ita ke maganin mai karya,inaso ka binkici wannan magana. Ya maigirma gwanna kahutawa sun fusata sunce POLIO akai kasuwa ba dai yayansuba domin wadanda ake neman kashewa mai nene shan inna domin hana yin wannan hanya kashe kahutawa ne. Kuma kahutawa basu da makiyin da yafi wanda ya da katar dayin wannan aikin hanya tasu. Ya maigirma gwamna daga cikin irin alkabain da ake dannawa akanka yan PDP wannan gari suke boye maka. Ka binciki ya kahutawa suke karashe wannan maganar (DAGA SAMA HAR KASA..........) kaji irin alkabain da jafain da tsinuwar da ake karasawa. Ya Maigirma gwamna gyara kayanka ba sauke muraba bane kum kukan kurciya jawabi ne. Ya maigirma gwamna mu daukacin matasa masu kishin cigaban kahutu barazanar wadanda sukaci amarka suka ki gayamaka gaskiyar halin dake ciki baza ta hana mu sanar dakai gaskiyar abin da ke faruwa ba. Domin musanka kai mai tausayin talakawa ne. Maigirma gwamna mu daukacin matasa masu kishin cigaban garin kahutu muna mika taaziyyarmu gareka Allah yajikan Daddijo Alhaji Shehu Shema yasa Aljanna tazama makoma amin.
Posted on: Sat, 16 Nov 2013 21:05:42 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015