Sabon Alamari ban fiya son daukar kiran private number ba - TopicsExpress



          

Sabon Alamari ban fiya son daukar kiran private number ba saboda tsaro, amma a wannan karin nayi mamaki dana tsinci dan yatsana yana yunkurin amsa kiran, a bari guda kuma ban hanashi aiwatarwa ba dan zuciya ta aminta da na dauka. Hello, kana lafiya? dodon kunnena ne ya jiyo amon muryar mace, na amsa a nutse; lafia lau nake, dan Allah lambar abokinka Lamare ko lamro nake so, nayi murmushi nace any way lamara kike nufi, yes tace dani, na maida mata amsar da fadin yanzu ina 2ra wani movie a wayana, in na gama insha Allah zan 2ro miki amma da da zaki bude lambarki, ko flashing kin min kinga nayi miki text a layin, abin mamaki sai ji nayi tace nagode tunda wulaqanci zakai min, nagode tunda ka hanani lambar sai anjima ta kashe wayar kafin nace wani abu. Allah sarki, mata kenan basa tsayawa su saurari bayani mutum mudin abinda suke nema ya gaza samuwa a lokacin, na fadawa abokina lamara bayan na bashi labarin abinda ya faru tsakanina da mai private number. Washe gari ina zaune wajen mai aski naje gyra gashi kaina, ina zaune ina sauraron faifan waqar Michael Jackson (billy jeans) wayana ta qara buga qugen tambarin kasata nigeria wanda shine kidan dake nuna alamat ana kirana, na fiddo ta daga aljifuna, dubawar da zanyi sai naga private number, na dauka nayi sallama, ta amsa min amma wannan karan ta sanyaya muryarta, a raina nace tofa yau kuma da wanne ta zo, kafin ta qara magana nace da ita bara na baki lambar Lamara din, abin mamaki tace dani tsaya Prince wannan kiran ba irin waccan bane, ba kuma lambar kowa nake so ba, in ma ka ban lambar ba inda zan rubuta. Nace mata toh! tayi dariya tace dani amma ka ban mamaki, ni nasan sunanka kai baka sani ba, ka kuma ki tambayar sunana, nayi murmushi nace da ita ai na san sunanki, ko mrs private number kenan ba na kashe wayar. Baa fi minti 2 ta qara kira tace dani mai kace sunana, na amsa mata da Mrs Private Number, tayi dariya tace lallai kam, ni dai sunana Zainab, kuma maabociyar karanta Post ne a wannan dandalin amma bazan fadama garin mu ko lambar wayana ba, don kunyarka nake ji, Allah sarki kunya sai kace wani siriiki nace da ita, wallahi haka kurum naji ina jin kunyarka ta fada min muryarta qasa_qasa. To kaji ina daf da gama rubutun nan sai wani kira ya shigo, abun mamaki kiranta shima da Private Number, hmm wai ta kira kurum ta gaisheni Mai karatu shin wane irin kunyata ce wannan? Kai nifa na kasa gane wannan alamrin ko zaku iya ganar dani? #Prince_Ahmad_Amoeva 2B0EEE99 08066038946
Posted on: Wed, 04 Dec 2013 20:07:45 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015