Sabon Salo Labari Na 5 Masoyiyata Ina Kike Ne??? (Kashi Na - TopicsExpress



          

Sabon Salo Labari Na 5 Masoyiyata Ina Kike Ne??? (Kashi Na 2) ...jikina yayi wani iri da naji abinda direban Taxin yace, nan take nai tunanin mai zai hana ince masa na fasa sauka? A can wani bangaren kuma sai naga cewa ai mata ba’a yi musu gaggawa, dan tabbas idan na fasa sauka budurwar zata san cewa saboda ita ne, ‘malam kai nake jira’ mai Taxin ya qara tunatar dani. Haka na daure na bude qofar motar na fito jikina duk yayi sanyi ganin murnata tana nema ta koma ciki, na fito na tsaya ina laluben qarya a cikin aljihunana a zuwan ina neman kudin da zan biya mai Taxi, dai dai lokacin da na miqa basa kudinne sai wani murmushi ya bayyana a fuskata ganin matsalar tawa ta warware a lokacin da ‘yar kyakykyawar budurwa ta miqo min dan qaramin katinta mai dauke da adireshi, dama ni duk tunina shine idan ta tafi a ina zan qara ganinta? Na karbi katin nata cikin murna sannan nima nasa hannu a aljihu dan in dauko nawa katin in bata, amma kafin in ciro mai Taxi yaja mota yayi gaba, ‘oho dai sai kai ta tafiya tunda na karbi nata’, nace a cikin zuciya lokacin da mai Taxi ya fizgi motarsa da gudu. Na juya kenan zan shiga layinmu sai naji an kira sunana ‘Abul Adfal!’, na waiga da sauri dan inga ko waye; wani tsohon abokina ne yake kira daga gidan gaban wata mota! Mun kai shekaru goma bamu hadu ba saboda kasancewar sun tashi daga garinmu sun koma wani gari, cikin mamaki na matsa kusa dashi ‘Jamil kaine yau a garin?’, ‘wallahi nine, Baban Yara kana duniyar nan? Ya gari ya iyali?’, ‘gari lafiya iyali kuma suna nan zuwa dai’ nace dashi cikin yaqe, ‘gashi kuma sauri muke Dad dina yana jira na a filin jirgi, bari in baka Katina sai muyi Magana daga baya’, Jamil ya dauko katinsa daga aljihun mota sannan yaci gaba; ‘sai dai wannan lambar da take jiki bata aiki bari in rubuta maka wacce nake amfani da ita yanzu...’, ya fara rubutun kenan sai na katseshi ‘bari in baka nawa nima sai ka kirani’, ‘to shike nan’ inji Jamil, na dauko katina daga aljihu na miqa masa sannan na karbi nashi, suka ja mota suka tafi ni kuma na gangara gida. Ina shiga gida na zarce dakina cikin sauri dan in samu in kira kyakykyawar budurwar dan inyi mata ban gajiyar komawa gida, nasa hannu a aljihu dan in ciro katin da ta bani, amma ga mamaki na sai naga katina ne a ciki, hantar cikina ta wani kada kululululu da na gane cewa ashe katin da yarinyar ta bani shi na bawa Jamil a matsayin katina, nan da nan na dauko katinshi dan na kirashi, sai kuma na tuna ai yace lambar da take jiki bata aiki! Sannan shi da ya kamata ya kira ni ba katin nawa na bashi ba! Can kuma sai nayi tunani wataqila shi zai kirata dan ta bashi lambata, damuwa ta sake kamani da na tuna cewa ai ita kuma dan Taxi bai bari na bata nawa katin ba, nayi gaggawar duba izuwa adireshin gidan su Jamil wai ko na bishi gida, af; ashe adireshinsa na Abuja ne yake jiki. Nan take na fada kan kujerar dake baya na nai zaman dabaro ina fadin MASOYIYATA INA KIKE NE??? Har na fara tunanin haqura sai kuma na tuna ai Jamil ya fara rubuta lambarshi a bayan katinshi, nan da nan nai duba izuwa bayan katin sai naga ya rubuta 070695902... wato lambobi biyu kawai ya rage lambar ta cika, sai naji na fara jin haushin kaina da na tsayar dashi bai gama rubutun ba. Can sai wani tunani yazo min, indai lambobi biyu ne kawai to ai dole su kasance daya daga cikin wandannan: 00,01,02,03,04,05,06,07,08,09,10,11,12,13,14,15,16,17,18,19,20,21,22,23,24,25,26,27,28,29,30,31,32,33,34,35,36,37,38,39,40,41,42,43,44,45,46,47,48,49,50,51,52,53,54,55,56,57,58,59,60,61,62,63,64,65,66,67,68,69,70,71,72,73,74,75,76,77,78,79,80,81,82,83,84,85,86,87,88,89,90,91,92,93,94,95,96,97,98,99, wato daya daga cikin dari, sai naga mai zai hana inyi ta daukar dai-dai ina gwadawa har in samo lambar Jamil ? Amma kuma sai naga aikin da wahala kuma zan kashe kudin kati da yawa, amma da na tuna kyawun yarinyar nan kuma na tuna cewa dama ba’a samun abu mai kyau haka ta sauqi, zumbur na miqe na fita naje na sayo katin N1, 500 nazo na fara kira, na fara da 07069590200, 07069590201, 07069590202, 07069590203. . . , haka na dinga kiran mutane daban-daban, wani lokaci naji muryar babba, wani lokacin yaro, wani lokaci mace, wani lokacinma sai naji muryar bayerabe ko inyamuri, wani yaren ma ban san me suke cewa ba, na dauki lokaci mai tsaho kafin daga baya nazo na sameshi a lamba ta 76 ; wato 07069590276, nai masa bayanin abinda ya faru yana ta yimin dariya, haka dai nasa ya karantomin lambar yarinyar dake jikin katin da yake wajensa, nan da nan na kirata…, wayar tana fara qara ta dauka, ‘Assalamu Alaikum’ nace da ita, sai tace ‘har na fara damuwa da naga kamar baza ka kirani ba zuwa tsahon lokacin nan’, nayi wani murmushin yaqe dana tuna abubuwan da suka faru bayan rabuwarmu da ita, ina mai cike da nishadin jin muryar kyakykyawar yarinyar, daga nan muka cigaba da fira kamar haka. . .KODAYAKE SOYAYYA SIRRICE BA SAI KUNJI ME MUKA CE BA KO?
Posted on: Sat, 06 Jul 2013 08:41:00 +0000

Trending Topics



height:30px;">
Make Your First $20 Online In The Next 24hrs Without Spending Any
ace check cashing dallas tx

Recently Viewed Topics




© 2015