Shugaban Amurka Barack Obama ya jinjinawa kasar Senegal - TopicsExpress



          

Shugaban Amurka Barack Obama ya jinjinawa kasar Senegal bisa kasancewa daya daga cikin kasashen da dimokradiyyarsu ta girku, tare da dorewar zaman lafiya da kwanciyar hankali. Da yake jawabi ga manema labarai a ranar farko ta ziyarar kasashe uku a Afirka, bayan ganawa da shugaba Senegal Macky Sall, Mr. Obama yace Senegal ta gudanar da zabuka na gaskiya da adalci da kuma mika sauyin ragamar mulki cikin lumana da zaman lafiya. Cikin batutuwan da shugabannin biyu suka tattauna sun hada da na tsaro a yankin Afrika ta yamma da kasuwanci. A lokacin jawabin nasa, shugaba Obama ya bayyana kasashen Saliyo da Liberia da Nijar da kuma Ghana, a matsayin wadanda suma tsarinsu na dimokuradiyyar ya samu gindin zama. *gb*
Posted on: Thu, 27 Jun 2013 16:56:42 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015