Shugabannin kasashen kungiyar tattalin arzikin Afrika ta yamma, - TopicsExpress



          

Shugabannin kasashen kungiyar tattalin arzikin Afrika ta yamma, ECOWAS ko CEDEAO sun fara taron yini biyu a Abuja, babban birnin Najeriya. Ana sa ran taron zai tattauna kan batun rikicin siyasa da kuma tsaro a Mali da kuma Guinea Bissau. Taron zai kuma duba wani daftari a kan Mali wanda mai shiga tsakani a rikicin na Mali a madadin ECOWAS, kuma shugaban Burkina Faso, Blaise Compaore da mataimakinsa shugaba Goodluck Jonathan za su gabatar. Kasar ta Mali dai na shirin yin zaben shugaban kasa a ranar 28 ga watan Yulin wannan shekarar.
Posted on: Wed, 17 Jul 2013 21:52:45 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015