TAMBAYA TA 635 ***************** MALAM INA NEMAN TAIMAKON ADDUA - TopicsExpress



          

TAMBAYA TA 635 ***************** MALAM INA NEMAN TAIMAKON ADDUA DA MAFITA, MALAM MATSALATA ITACE NIDAI NA KASANCE MACE MAI TSANANIN ZAFIN RAI MAI KUMA SAURIN FUSHI KUMA DUK YAYINDA RAINA YA BACI INA YAWAITA HUKUNCI CIKIN FUSHI WANDA DAGA BAYA SAI NA DAWO INA DANASANI, KUMA SAURAN HALAYENA BABU LAIFI DOMIN MAMANA TANA CEWA BADAN ZUCIYA DA FUSHIBA DA NA ZAMA DAYA DAGA CIKIN MATA NAGARI KUMA GASHI NA KUSA AURE, INA TA ADDUA AMMA BAN DAINABA, SHINE NAKE SO DON ALLAH MALAM A BANI ADDUA KO SHAWARA KODAI WANI DAUKI DAZAN SAMU MAFITA, DON GIRMAN ALLAH MALAM A TAIMAKAMIN. (Daga wata Baiwar Allah) AMSA ****** Hakika saurin fushi yana daga cikin mugayen dabiu wadanda musulunci yake nuna mana mu gujesu. Wani mutum yazo yace wa Manzon Allah (saww): YA RASULALLAHI (ina son) KAYI MIN WASIYYA Shi azatonsa Annabi (saww) zai zaunar dashi yace masa yi kaza kabar kaza ko yai masa wasu jawabai masu tsawo. Amma da yake MANZON NAMU (saww) Allah ya azurtashi da JAWAMIUL KALIMI (wato kalmomi yan kadan masu tattarowa maanoni da yawa). Sai yace masa: KAR KAYI FUSHI (Sahihin hadisi ne yazo ta hanyoyi fiye da biyar ingantattu) Me yasa Annabi (saww) yace masa kar yayi fushi? Sai malamai sukace saboda fushi yana daga cikin MANYAN KOFOFIN DA SHAYTAN YAKE SHIGOWA TA CIKINSU DOMIN YA HALLAKAR DA BIL ADAMA. Fushi mummunar Dabia ne wadanda akullum yake jefa maabotansa acikin Baqin ciki da nadama da hasara da gaaba da yan uwa, da yanke zumunci da kiyayya da munana zato. Sau da yawa mukan gani idan shaitanun aljanu sunyi sunyi sun kasa shiga jikin bil adama, sukan koma gefe ne su jirashi sai lokacin da yake cikin fushi sannan su samu nasarar shiga jikinsa. Fushi yana kore mutum daga samun yardar Ubangiji. Fushi yana hana mutum samun nutsuwa azuciyarsa. Kuma yana hana mutum aikata alkhairi. Don haka ki yawaita karatun Alqurani da sauraronsa ko yaushe. Insha Allahu zaki rika jin sanyi azuciyarki. Sannan ki rika yawaita bibbiyar tarihin magabata na kwarai domin daukar darasi aharkokin rayuwa. Ki rika karanta wannan adduar ta Annabi Musa (as) RABBISH RAH LEE SADREE WA YASSIR LEE AMREE Insha Allahu zaki samu saukin zama da mijinki. Ki rika karanta wannan adduar: ALLAHUMMAJ ALNEE SABIRATAN WAJALNEE SHAAKIRAH Da kuma adduar Nana Aisha (rta) ALLAHUMMA INNAKA AFUWWUN KAREEMUN TUHIBBUL AFWA FAAFU ANNEE Ya Allah ka gyara mana zukatanmu mu zama masu biyayya agareka ko yaushe.
Posted on: Tue, 15 Oct 2013 01:45:05 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015