TAMBAYA TA 639 *************** Mallam wata damuwa ce dani. wani - TopicsExpress



          

TAMBAYA TA 639 *************** Mallam wata damuwa ce dani. wani lokacin idan ina fitsari a karshen fitsarin sai wani ruwa yallow yallow mai kauri yana fitowa ta Gabana, kuma akwai wasu kwayoyi acikinsa sannan kuma yana da yauki. kamar ruwan maniyyi amma dai ban san menene ba. yakan fito min idan ina yunkurin yin fitsarin kuma gabana yana tattarewa amma ba koyaushe yake min ba. wani lokacin ma yakanyi kamar siti 2.. dan Allah mallam a temaka min da magani, ko shawara. nagode. (daga wani bawan Allah) AMSA ***** Ai wannan abinda yake fita daga gabanka sunansa WADIYYI. Kuma yana fitowa ne a farko ko kuma Qarshen fitsari. Hukuncinsu daya ne da fitsarin. Wankeshi kawai zaka yi.. Ban san wani maganin da ake sha domin kar ya fito ba.. Iyakar sani na dai fitowarsa yanayin halitta ne ba larura bace. Amma acikin mutanen #ZAUREN_FIQHU idan akwai wanda yake da maganin sai ataimaka.. WALLAHU AALAM.
Posted on: Thu, 17 Oct 2013 19:10:19 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015