TAMBAYOYI GUDA 50. Muna cikin wani zamani da Mutane Sunfi Damuwa - TopicsExpress



          

TAMBAYOYI GUDA 50. Muna cikin wani zamani da Mutane Sunfi Damuwa da Bayani akan wasu fiye da kansu sunfi binciko laifin wasu fiye da Nasu SAYYIDINA UMAR yace kuyiwa kanku Hisabi kafin ayi muku abubuwan da suke kawo tsira bautawa Allah shi kadai da iklasi akan sunnar Manzo Allah a cikin akida da ibada da Muamulah da Halaye Masu kyau yiwa kanka TAMBAYA 50 don kasan Matsayinka: Allah yasa Mu dace; 1.waye ya yika? 2.Mai yasa ya yika? 3.kai waye? 4.A ina kake? 5.Mai kake yi? 6.Ina zaka? 7.Mai zai faru? 8.Mai kafi so a rayuwarka 9.Mai kafi ki a rayuwarka 10.Duk abinda kake yi kana da Hujja a Sharia? 11.Su waye abokanka? 12.Yaya zamanka da iyayenka? 13.Yaya zamanka yake da iyalanka? 14.Wace kungiya kake yi don me? 15.Akwai wani yanzu haka da bakwa shiri da shi? 16.Tsakani da Allah ka taba cin Amanda? 17.Kana yin karya? 18.kana Dunguma Ashar? 19.Yaya zamanka da Makwabtanka? 20.Wace shedar ilimi kake da ita? 21.kana salloli a jami Musamman a Masallaci? 22.Yaya alakar ka da Danginka take? 23.Shi kana sada zumunta? 24.Shin kana bayar da Sadaka? 25.Shin karanta Alqurani Mai girma? 26.Kana azumin litinin da Alhamis? 27.Kana sallar Shafai da wuturi? 28.Kana zuwa Assibiti domin ziyarar Marassa lafiya? 30.Shin kana Kwanaki masu haske, ranar sha ukku,sha hudu,Da sha biyar? 31.shin kana kiyamul laili? 32.Kana Umarni da kyakyawa da hani da Mummuna? 33.Kana zuwa aiki a kan kari kuma ka tashi a kan lokaci? 34.Kana zuwa gaban MALAMI domin daukar karatu? 35.ka tabbatar abinda kake ci halan ne? 36.kana kuwa Damuwa da halin da yan uwanka Musulmi suke ciki? 37.kana taimakon Marayu kuwa? 38.Salati nawa kake yiwa Annabi S.A.W kullum? 39.Istigfari nawa kake yi kullum? 40.kana zuwa Makabarta domin tuna lahira? 41.Kana zuwa taaziya da sallar janaiza? 42.ka taba yin kuka saboda tsoron Allah? 43.Shin kana yiwa dukkan musulmi sallama ko kuwa sai wanda kassani? 44.Kanayin Rantsuwa akan karya kuwa? 45.kana shan taba ko wiwi ko giya ko hodar iblis? 46.Kana jin kade-kade da wake-wake? 47.Kana Aske gemunka? 48.Ka taba karbar cin hanci 49.Kana kyautatawa iyalanka? 50.Kana GABA da wani kuwa? Pls.forward it to some. THANKS. SHIN KA TABA TSAYAWA KAYI TUNANIN MUTUWARKA ??
Posted on: Tue, 05 Nov 2013 10:21:44 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015