TARIHIN NANA AISHA KASHI NA UKU - TopicsExpress



          

TARIHIN NANA AISHA KASHI NA UKU Allah ya taimake ni suka daukeni aikin koyarwa da turanci,ina cikin koyarwar sai akabani shugabar makarantar firamare ta FCE (demonstration school).Bayan mijina yasake samun aiki a Abuja a hukumar kula da kan iyaka (boundary commission) sai nabar FCE Gombe,nakoma Abuja,alokacin anbude sabuwar kwalejin ilimi ta Zuba,sai na nemi aiki asabuwar kwalejin,nan ma suka daukeni aiki.ina cikin koyarwar sai suka bani shugabar sashin yarurruka(HOD Languaages)na kwwalejin.Daga nan sai akabani shugabar kwamitin shugabannin manyan malamai(chairperon commitee of deans)rashin mataimakin shugabar kwalejin,sai aka bani riko wato (acting Deputy Provost).Bani wannan shugabancin yasa ina rike da mukamai uku kenan,wato na shugabar sashin yarurruka da shugabar kwamitin shugabannin malamai da kuma mukaddashiyar shugabar kwalejin na riko,banjima akan wannan mukami ba,sai nasamu takarda an kirani inkoma Gombe anbani kwamishiniyar ilimi.
Posted on: Sat, 05 Jul 2014 23:18:45 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015