TIRELA TA MARAKADE WATA MACE DA JARIRINTA A KANO. A karshen makon - TopicsExpress



          

TIRELA TA MARAKADE WATA MACE DA JARIRINTA A KANO. A karshen makon jiya ne tirela ta markade wata mace da jaririnta a kofar Famfo kusa da tsohuwar Jami’ar Bayero da ke Kano. Wasu ganau sun shaida wa Aminiya cewa lamarin ya faru ne a daidai lokacin da aka tsayar da motoci, sai dai kuma sakamakon lalacewar birkin tirelar sai direbanta ya kasa tsayar da ita inda ta yi kan wata mota kirar Golf da wani keken A Daidaita Sahu da ke tsaye a kan titin. An ce karar dukan da tirelar ta yi wa motocin ne ya sa matar da ke cikin keken A Daidaita Sahun ta fito a guje da niyyar neman tsira, inda motar ta markade ta da jaririn da take goye da shi. “Matar tana fitowa daga ‘ A Daidaita Sahun” sai motar ta yi kanta nan take ta markade ta da jaririn da ke goye a bayanta, sai zaro su aka yi daga jikin motar sakamakon makalewa da suka yi,” inji majiyarmu. Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano ASP Magaji Musa Majiya ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce tuni aka bayar da gawar matar da ta danta ga ’yan uwanta don yi musu jana’iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada. Majiya ya ce rundunar ta kama direban tirelar, kuma da zarar ta kammala bincike za ta gurfanar da shi gaban kotu. (Aminiya)
Posted on: Sun, 06 Oct 2013 11:20:51 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015