TUNDA NAKE BANKO TABAJIN LABARI MAI TAUSAYI IRIN WANNAN - TopicsExpress



          

TUNDA NAKE BANKO TABAJIN LABARI MAI TAUSAYI IRIN WANNAN BA........... Wata rana wani mutum ya sayi sabuwar mota daga sayanta yaxo kofar gida yai packng, bayan ya shiga gida ya fito sai ya tarad da dansa yana rubutu a jikin motar tasa nan take uban yaron ya hau yaron da bugu kamar xai kasheshi akan yayimai rubutu ajikin mota... Ya kama yaron ya daure masa hannuwa ta baya yayimai dauri GORO, yadaukeshi ya saka a wani daki ya kulle ya tafi da dan mabudin... Uwar yaron tanata kuka tarasa yadda xatayi ta bude dakin ta kwanceshi,haka tanaji dan nata yana kuka tun yana kuka har yagaji ya daina... Bayan wani lokaci mai tsawo uban xuciyarsa ta sauko sai yadawo domin ya kwance yaron koda ya bude dakin ya sami dan nasa a sume ko motsi baya iyayi,nan take ya daukeshi xuwa asibiti.. Bayan likitoci sun kammala bincike sai suka shaidawa ubanyaron cewa sai an yanke hannuwan yaro sakamakon dadewa da yayi a daure...haka uban yasa hannu a takarda aka yanke hannuwan dan nashi... Bayan wani lokaci yaron ya farfado daga aikin da akayi masa sai uban nasa ya shigo domin yaga dan nasa yana shigowa suka hada ido da yaron,sai yaron ya fashe da kuka yace BABA DAN ALLAH KAYI HAKURI KA DAWOMIN DA HANNUNA BAZAN KARA MAKA RUBUTU A JIKIN MOTAR KABA.. nan take da uban da likitoci da duk wanda ke wajen kowa ya fashe da kuka.. Bayan mutumin yafita waje sai ya tsaya ya kalli rubutun da dan nasa yayi da kyau sai yaga yaron ya rubuta I LOVE U DADDY nan take uban ya kara fashewa da kuka. **** ya yan uwa murinka kokarin yafawa xuciyarmu ruwan sanyi a yayinda ranmu ya baci,mu sani cewa dokin xuciya ba inda yake kai mutum sai ga halaka. Allah yasa mufi qarfin xuciyanmu.
Posted on: Tue, 22 Oct 2013 08:04:43 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015