TUTAR MASARAUTAR BAUCHI A cikin shekarar 1948 aka maye sandar - TopicsExpress



          

TUTAR MASARAUTAR BAUCHI A cikin shekarar 1948 aka maye sandar girma (Staff of office ) da tuta domun kafin wannan lokaci duk yadda Sarki zai je da wannan sandar yake tafiya. A dai dai zamanin Sarkin Bauchi Yakubu Dan Umaru shine ya fara amfani da wannan tutar a kofar Fada da kuma gaban motar sa, amma kafinnan Sarkin bauchi Yakubu me gari shi ya fara amfani kuma da staff of office. Ana daga wannan tutar da safe misalin karfe shida a kuma sauke da yamma misalin karfe shida. Duk lokacin da aka zo dagawa ko sauke wa akwai mutumin da aka ajiye domun yin busan bigila me suna Zailanin Bar wanda aka fi sani da Baba Busa. . . Wannan tutar tana da launi har uku kuma ko wani launi yana da nashi manufar, sannan a tsakiya akwai wata da tauraro guda uku. Launin farko a sama shi ne rawaya (yellow) wannan launi an fassara ta ne da farin ciki da kwarin gwuiwa da sadaukarwa. Launi na biyu fari ne (white) an fassara ne da tsarki. Launi na uku shine shudi (blue) an fassara ne da Yanci da hadin kan alumma. Bisa wadannan fassara dukkan wadannan fassarar da aka yi wa tutar Marasautar Bauchi ya tabbata gareta. dai dai anyi mata fassara da yadda kasar da Masarautar take. Wata kuwa haske ne na Shehu Tauraru kuwa manyan Sarakunan Daular da kuma yadda ko wane ya tsare, Yakubu shi ne a gaba kuma ya tsare kudancin Daular Bello kuwa gabashi Abdullahi kuwa Yamma.
Posted on: Tue, 18 Nov 2014 06:18:28 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015