Tabbas IBLIS YANA RUDAR DA TUNANIN MUTANE! ALLAH KABAMU - TopicsExpress



          

Tabbas IBLIS YANA RUDAR DA TUNANIN MUTANE! ALLAH KABAMU KARIYA!!! SAKO DAGA SHAIDAN !!! Barkanku da war haka! Sunana # Iblis_dan_Lis , Jagoran masu sharholiya da sheke ayarsu, Na girmi mahaifin Yan Adam balle Annabawa da Manzanni, Na kuma zauna acan Sama, yau kuma gani a kasa, Na shiga Aljanna na kuma ga wuta da idona, Saboda haka ban ga abin tsoro ba, don mu muka san Jiya balle Yau. Na san ana fada muku cewa ni Makiyinku ne ko??? Amma yaya makiyinku zai nusar da ku kan abinda zai sanya rayuwarku anan Duniya cikin Holewa da morewa da fantamawa ??? Ina kiranku ku biyoni muci Duniyarmu da tsinke!! Na san abinda ake tsorata kuda shi itace Wutar Jahannama, To ai Manzon Allah yace cikin Mutum dubu daya ne kawai zai shiga Aljanna, Jahannama mai tsallaketa a wannan Zamanin yan kadan ne!!, Kar ku damu abin Ruwan dare ne, kuma gobara ce a kasuwa. Ina kira ga # Mata manyan kwamandojina, Da ku kara himma, ku samo mana mabiya,don ina alfahari da kokarinku na samo abokan zama a wuta, sama da kokarin sauran tawagata, Ku rudesu ku batar da su, kuyi shigar ashararanci, Ku dauke musu hankali, Sannan ku kuma ku sheke ayarku a gidajen Biki, kar ku kyale lokacinku ya amfaneku,kuy Kalle kalle don nishadantarwa, ku bata lokacinku a kansa, Naji ance ma wani sabon kaset ma ya fito ko?? # Malamai_ yan_tsubbu da masu adduar sayarwa, na san ana kokarin 6ata tsakanimmu, waikuma na Allah ne, Kar ku damu!! Ni nasan gudummawar da kuke bayarwa kan wannan Tafiya ta fi gudummawar masu # Gidan_Giya da mafi yawan Mabarnata, domin hanyarku da wahala a tuba, Gani ma ake yi bautar Allah kuke yi, don na riga na kawata muku wannan turba, sannan ga wahayin rubabbun hujjoji da na ke muku a kodayaushe, amma sauran masu sabo sai kaga mutum ya jima ana gwagwarmayar nan da shi sai kaji kwatsam wai ya tuba!!Amma ku kam da wahala irin haka ta faru domin baku jin cewa zunubi kuke aikatawa. Kar ku damu, In munje Lahira kuce ni na batar daku, Na daukar muku alkawarin baku kowace irin kariya, sai dai in wuri yayi wuri zan ce ban taba saninku ba, In Lamari ya tsanani, wiri yayi wuri, Iya ruwa ne fidda kai!! A karshe kun san ai makomarmu da ku wuta ne, Na kuma san bamu da rabo a lahira, amma kam!! Ai muna sheke ayarmu anan Duniya gabanin muje can Lahira a shigar damu wuta. Daga Makiyinku abokin gabarku Shaidan Bye Bye sai an jima!!!!!! KUKAN KURCIYA....
Posted on: Wed, 06 Nov 2013 05:21:45 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015