Tambayoyi zuwa ga dan Shia Addinin shia ta kafirtar da - TopicsExpress



          

Tambayoyi zuwa ga dan Shia Addinin shia ta kafirtar da khaleefofi ukun bayan Sayyidina Aliy, Wato Abubakar,Umar, Usman (Allaah ya kara yarda dasu) Kuma sun zayyana wannan mumunar maganar a cikin littafan su, Irin su Alkaafi, da kashful Qhumma, Bihaarul Anwar d.s . Lallai ya tabbata a hadithin Saeed ibn Jubair manzon Allaah(s.a.w) yace: Mutane goma daga cikin quraishawa yan Al-jannah ne: Ni ina cikinsu,Abubakar ma dan Al-jannaa ne,Umar ma dan aljannaa ne,Uthman ma dan aljannaa ne, Aliyu Ma dan aljannaa ne. Wa anda suka ruwaito wannan hadithin sune: Imamu Ahmad(1/188),Abu dawood(4649),Tirmidhi(3757). Harwa yau Allaahu s.w.t yana cewa game da sayyidina Abubakar a cikin alquraani mai girma,inda yake cewa: Kuma mafi taqawa zai nisance ta,Wanda yake bayar da dukiyarsa, alhalI yana tsarkaka. (Q92:17-18) Anan Allaah yana nufi sayyidina Abubakar zai nisance wuta kasancewar dukiyansa da bayar wurin fansar sayyidina Bilal. Tambaya Anan: Ya akayi manzon Allaah ya tabbatar masu da aljannan bayan kafirai ne a cewar ku? Ko dai harda kafiri yana shiga Aljannan? Ashe ba duk maganganun manzon Allaah wahayi ne ba, ko baku karanta zancen Allaah bane ba a suratul Najmi? Ya akayi Allaah ya yabe su bayan yasan zasuyi ridda,tunda shi masanin gaibu ne? Allaaah ya kiyaashe mu daga bata...aameen.
Posted on: Wed, 20 Nov 2013 16:37:49 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015