Tarihin Imam Hasan Al-Mujtaba (a.s): ________________________ Shi - TopicsExpress



          

Tarihin Imam Hasan Al-Mujtaba (a.s): ________________________ Shi ne babban jika, al-Hasan bin Ali bin Abi Talib. Mahaifiyarsa ce Fatima al-Zahra da tarihinta ya gabata. Daga abubuwan da muka ji na tarihin mahaifin shi (Imam Ali) da mahaifiyarsa (Zahra) nasabarsa da wannan madaukakin dangane ta gama bayyana. Matsayinsa(AS) Kamar sauran kebabbun ‘yan-gidan Manzo (SAWA), Imam Hasan (AS) na da madaukakiyar daraja a wannan addini. Musulmi ba sa sabani a kan cewa ayar tsakakewa ta kunshe shi, haka ayar ciyarwa, ayar kauna da ayar Mubahala ; wadanda duk ambatonsu ya gabata. A bakin Annabi (SAWA) kuwa an ji zantukan kauna, girmamawa da daukakar matsayin Imam Hasan daga gare shi. Bukhari da Muslim sun riwaito daga Barra’u bin ﺃzib, ya ce: Manzon Allah (SAWA) ya kasance yana dauke da Hasan bin Ali a kafadarsa alhali yana cewa: Ya Allah ina sonsa, don haka Kai ma Ka so shi.[1] Anas bin Malik ya ce: An taba tambayar Manzo (SAWA) cewa daga mutanen gidanka wa ka fi so? Sai yace: “Hasan da Husaini”. Ummul-Mu’uminin A’isha ta ce: Manzon Allah (SAWA) ya kasance yana daukar Hasan ya rungeme shi sannan yakan ce: Ya Allah wannan dana ne, kuma ni ina sonsa, to Kai ma Ka so shi, Ka kuma so mai sonsa. Jabir bin Abdullah al-Ansari ya ce: Manzon Allah (SAWA) ya ce: Wanda ke son ya kalli shugaban matasan Aljanna sai ya kalli Hassan bin Ali. Imam al-Ghazzali ya fitar da cewa: Manzon Allah (SAWA) ya cewa Hasan (AS): Ka kamantu da ni a halitta da dabi’u.[2] A wani wajen an riwato Annabi na cewa: Hasan da Husaini Imamai ne sun mike (sun yi yaki don tabbatar da haka) ko sun zauna (ba su yi yaki ba).[3] Haihuwarsa(AS) An haifi Imam Hasan (AS) a ranar sha biyar ga watan Ramalan mai albarka, shekara ta uku bayan hijira. Farin ciki mai yawa ya lullube gidan Fatima da samun wannan abin haihuwa mai albarka. Nan da nan aka je aka yi albishir ga Manzo (SAWA). Manzo ya yi matukar farin ciki da wannan abin haihuwa, nan da nan ya zo ya dauke shi ya rungume shi sannan ya yi kiran sallah a kunnen shi na dama, ya yi ikama a na hagu. Sannan ya dubi Imam Ali (AS) ya tambaye shi ko wane suna ya zaba masa. Imam ya ce: ‘Ai bai kamata in gabace ka ba ya Manzon Allah’. Sai Manzo ya ce: haka ni ma ba na gabaci Allah ba’. Wannan muhawara ba a dade da gama ta ba sai ga wahayi daga Allah na saukowa inda ake sanar da Annabi cewa: ‘Hakika Allah Ya yiwa abin haihuwa mai albarka sunaHasan ’.[4] Bayan kewayowar kwana bakwai da haihuwa: Sai Manzo ya yi masa akika da babban rago, ya ba unguwar zoma cinya daya da dinari daya don godewa kokarinta.[5] Dabi’u Da Halayensa(AS) Jikansa Imam al-Sadik (AS) ya bayyana halayen Imam Hasan (AS) da cewa: Hasan bin Ali ya kasance ya fi duk mutanen zamaninsa ibada, kuma ya fi su gudun duniya kuma shi ne mafificin su. [6] Har ila yau Imam al-Sadik (AS) ya ce: Hasan bin Ali (AS) ya tafi aikin hajji sau ashirin da daya a kafa… [7] Ya kasance idan yana alwala sai a ga launinsa ya canza kuma gabubbansa na kakkarwa, sai aka tambaye shi dalilin haka, shi kuwa ya ba da amsa da cewa: Hakki ne a kan duk wanda ya tsaya a gaban Ubangijin Al’arshi launinsa ya canza, kuma gabubbansa su kada.[8] Ya kasance mai yawan taimakon mutane, ta yadda babu wanda zai tambaye shi wani abu face ya ba shi. Wata rana aka tambaye shi mai yasa koda yaushe aka tambaye shi abu sai ya bayar, sai ya amsa da cewa: Hakika ni ma mai rokon Allah ne, kuma mai kwadayi gare Shi; don haka ina kunyar in zama mai roko alhali kuma ina hana mai roko. Kuma Shi (Allah) Ya sabar da ni da bayar da ni’imarSa gare ni, haka ni ma na sabar da Shi in bayar da ni’marSa (da Ya ba ni) ga mutane; to ina tsoron in na yanke al’adata Shima Ya yanke al’adarSa.[9] Imami Dan Imami A lokacin rayuwar mahaifinsa, Imam Hasan ya kasance, ba kawai da mai biyayya ba ne, har ma jami’i ne mai da’a. Ya halarci dukkan yakokin da mahaifinsa ya yi da azzalumai a Basra, Seffin da Naharwan; ya kuma taka muhummiyar rawa wajen kashe wutar fitina; ba don komai ba sai don kare Musulunci da mutanensa. Ya kuma wakilci mahafinsa a wurare da daman gaske. Kafin Imam Ali (AS) ya bar duniya ya yi wasici a Imam Hasan (AS) a matsayin Imam. Ga abin da ya fada a lokacin da bakinsa: Ya kai dana, hakika Manzon Allah (SAWA) ya hore ni da in yi wasici da kai kuma in ba ka littafaina da makamaina kamar yadda shi ya yi wasici da ni kuma ya ba ni littafansa da makamansa. Haka ya hore ni da in hore ka da cewa idan mutuwa ta zo maka ka bayar da su ga dan’uwanka Husaini. Sannan ya waiwaya ya dubi Husaini(AS) ya ce: Manzon Allah (SAWA) ya hore ka da ka bayar da su ga wannan dan naka… Sai ya kama hannun Imam Ali Zainul-Abidin(AS) ya ce: Kai kuma Manzon Allah (SAWA) ya hore ka da ka bayar da su ga danka Muhammad; ka isar da gaisuwa gare shi daga Manzon Allah da ni.[10] Bayan shahadar Imam Ali (AS), a lokacin da Imam Hasan (AS) ya fito yana yiwa mutane huduba, yana sanar da su babbar masifa (ta rashin Imam); bai ko gama ba sai Ibin Abbas ya fara kiran mutane da su mika masa bai’arsu. Haka kuwa abin ya kasance, aka yi wa Imam Hasan Mubaya’a a matsayin Khalifa. Labarin bai’ar da aka yiwa Imam Hasan ta girgiza Mu’awuya kwarai da gaske, don haka ne ma ya kira taron gaggawa tare da masu ba shi shawara a kan harkokin siyasa don samo hanyar da za a fuskanci sabon yanayin da aka shiga. Masu taron sun dace a kan a dauki matakin watsa ‘yan leken asiri cikin garuruwan dake karkashin shugabancin Imam Hasan (AS), don cusa tsoro da yada karairayi don yin bakin fyanti ga hukumar Ahlulbaiti (AS). Haka taron ya bukaci da jam’iyyar Umayyawa ta fadada aikin jan hankulan shugabannin kabilu a Iraki, ta hanyar watsa rashawa da alkawuran karya da kyaututtuka da barazanoni da wasun wadannan.[11] Sai dai kafofin tsaron gwamnatin Imam Hasan sun iya gano wannan makirci tun bai je ko’ina ba. Wannan ne ya haifar da musayar wasiku tsakanin Imam da Mu’awuya, amma hakan bai yi amfani ba; domin Mu’awuya ya dage a kan ci gaba da hamayya. A karshe dai ya zama dole ga Imam Hasan (AS) ya shirya yaki da Mu’awuya; don haka ya fitar da bayanin da aka watsa mai cewa: Bayan haka, lallai Allah Ya wajabta jihadi a kan bayinSa Ya kira shi da abin da ba a so . Sannan Ya cewa Ma’abuta jihadi daga Muminai: Ku yi hakuri, lallai Allah na tare da masu hakuri. Ya ku mutane, ba za ku iya samun abin da kuke so ba sai da hakuri da abin da ba ku so. Ku fita –Allah Ya yi muku rahma- zuwa rundunarku a Nakhila …. [12] Sai dai kunnuwan da wannan sako na Imam ya shige su sun riga sun fara tasirantuwa da kage-kagen Mu’awuya, don haka ba su yi kazar-kazar wajen amsa kiran jihadi ba. Duk da haka wasu Muminai sun amsa wa Imam, suka tafi Nakhila –wani wuri dake wajen Kufah a kan hanyar zuwa Sham- don kama hanya zuwa arangama da miyagu. A kan hanya ne, ana shirin yak,i sai irin tasirin aikin Mu’awuya ya fara bayyana cikin rundunar Imam Hasan (AS), wanda daga baya ma har ya gane akwai wadanda ke jira a fara yaki su kama shi su kai wa Mu’awuya cikin sauki ya san yadda zai yi da shi. Don haka sai ga sanarwar dakatar da yaki daga Imam Hasan (AS). Wannan yanayin ne ya sa Imam Hasan ya amsa shirin sulhun da Mu’awuya ya yi kira da shi cikin wani mummunan yanayi. Yanayin da yaki ba zai taimaka wajen gyara shi ba sai ma dai kara gurbata al’amurra. Imam ya fadi dalilin karbar sulhun da ya yi da cewa: Wallahi da na yaki Mu’awiya da sun riki wuyana har sun mika ni zuwa gare shi cikin ruwan sanyi. Wallahi in yi sulhu da shi ina madaukaki* ya fi min a kan ya kashe ni ina fursunan yaki; ko ya yi min gori, (hakan) ya zama abin zagi ga Banu Hashim.[13] Ya kara da cewa: Ban zama mai kaskantar da Muminai ba; sai dai ni mai daukaka su ne. Ba wani abu na yi nufi da sulhuna ba face kau da kisa daga gare ku yayin da na ga sandar Sahabbaina da nokewarsu daga yaki. [14] Har ila yau ya taba fadawa Abu Sa’id cewa: Ya kaiAbu Sa’id, dalilin sulhuna da Mu’awuya shi ne (irin) dalilin sulhun Manzon Allah da Bani Dhamrah da Bani Ashaja’a da mutanen Makka, a lokacin da ya koma daga Hudaibiyya.[15] Sulhun Imam Hasan Da Mu’awuya Abin da wannan yarjejeniya ta kunsa shi ne cewa shi Mu’awuya ya yi aiki da Littafin Allah da Sunnar ManzonSa. Haka sulhun ya tanadi cewa kar Mu’awuya ya nada kowa a matsayin mai jiran gadonsa. Kuma Mu’awuya ya dauki alkawari tsakanin shi da Allah cewa ‘yan Shi’ar Ali za su zama cikin aminci na rayukansu da dukiyoyinsu, matansu da ‘ya’yansu. Sai dai tun farko Imam Hasan (AS) na so ne ya fitar da hakikanin Mu’awuya kowa ya gan shi ta hanyar wannan sulhu. Wannan kuwa shi ne abin da ya faru; domin Mu’awuya ya sabawa duk tanaje-tanajen sulhun. Bai yi aiki da Littafin Allah da Sunnar Manzo ba, kuma ya rika kashe bayin Allah da zababbun wannan al’umma, ya rika zaluntarsu da kwace dukiyoyinsu, ya watsa fasadi mai yawa a doron kasa. A Kufah ne Mu’awuya ya mikeya yi hudubar nan tasa da ya bayyanawa duniya ko shi wanene; yayin da ya ce: Wallahi ni ban yake ku don ku yi sallah ko azumi ko hajji ko zakka ba, domin ai kuna yin haka; na dai yake ku ne don in mulkeku, hakika kuma Allah Ya ba ni hakan alhali ku ba ku so. To ku saurara duk wani jini da aka zubar a wannan fitina ya tafi a banza, kuma duk wani alkawari da na dauka yana karkashin kafafuwan nan nawa guda biyu[16] Bayan sulhun ne Imam Hasan ya kuduri aniyar komawa Madina gefen Kakan shi (SAWA), ya koma can ya ci gaba da aikin shi na Imamanci (wanda ba ya kwatuwa). Inda ya koma ya shiga ja-gorancin tunani. Hakika kuwa zamansa na Madina bayan sulhun ya haifar da manyan masana Musulunci da gawurtattun masu riwayar hadisi. Zuwa MihrabinAllah Mahukuntan Umayyawa ba su zama cikin jahilcin ma’anar komawar Imam Hasan Madina ba. Suna sane da cewa zai koma ne wajen yada addini. Wannan ma babbar matsala ce gare su. Don haka sai suka fara makiricin raba shi da duniya. Amma sai suka fara daukar matakan siyasa kafin aiwatar da wancan mummunan kuduri na su na karshe. Matakin farko shi ne kuntatawa ‘yan Shi’ar Ali (AS), suna Koran su, suna toshe hanyoyin abincinsu, rushe giajensu da sauran irin wadannan. A kan haka gwamnatin Umayyawa ta sami taimakon miyagun gwamanoninta da jam’ianta irin su Mugirah bin Shu’ubah, Samrata bin Jundubi da Zaiyad bin Abihi. Ziyad ya kasance dan zina ne, don haka ne ma ake kiran shi Ibin Abihi (dan babansa), kuma shi ne gwamnan Umayyawa a Iraki. Mugu ne na karshe, tarihi ya hakaito cewa: Ziyad ya rika bin ‘yan Shi’ar Ali bin Abi Talib yana kashe su ko’aina har sai da ya kashe talikai masu yawa daga cikin su. Ya shiga yanke hannuwansu da kafafunsu, yana tsire idanuwansu. Ya zama yana rudin Mu’ayuwa da –samun kusanci da shi- da kashe su.[17] Haka Mu’awuya ya yi amfani da wasu masu wa’azozi masu mika wilaya ga masu mulki, wajen gurbata tarihin Ahlulbaiti masamman Imam Ali (AS). Abu Huraira –mashhurin mai riwayar hadisan nan- ya yi matukar taimaka musu a wannan fagen. Mu’awuya ya sa zagin Imam Ali (AS) ya zama al’ada a bisa mumbarorin Musulmi da hudubobin juma’a. Banda hadisan karya da ya sa aka yi ta cusawa kasashen Musulmi masu batanci ga addini da wadanda za su mara masa baya. Wadannan hadisai na Mu’awuya har yanzu suna nan cike da littafan Musulmi, masamman Ahlulsunna, suna aiki da su a matsayin hadisan gaskiya, alhali mafi yawan su ba su sani ba. Karshe shirin su shi ne kashe Imam Hasan (AS) da guba da Mu’awuya ya shayar da shi ta hanyar matarsa (Imam din) wadda ake kira Ja’adatu. Wadda kuma Mu’awuya ya rude ta, ya hure mata kunne, bisa alkawarin cewa daga baya zai aurar mata da dansa Yazidu.* Imam Hasan ya sha gubar ne cikin madarar da ya yi bude baki da ita bayan ya kai azumi. Ya rika yin tari har hantarsa na fitowa ta bakisa. Inna lillah Wa inna Ilaihiraji’un. Shahadarsa ta kasance a ranar bakwai ga watan Safar, shekaru hamsin bayan hijirar Kakansa (SAWA). Imam Hasan ya yi wasici da a bisne shi a kusa da Kakan shi Annabi. Sai dai Umayyawa, karkashi ja-gorancin Marwan bin Hakam, sun hana a bisne jika a kusa da Kakansa kuma masoyinsa, shugaban samarin gidan Aljanna. Don haka sai aka bisne shia Baki’a kusa da kabarin kakarsa Fatimatu bint Asad, mahaifiyar Imam Ali (AS). Amincin Allah ya tabbata gare ka a raye da mace, ya kai Abu Muhammad wanda aka zlunta. Imam Hasan ya rasu ya bar ‘ya’ya da dama; kuma wasu daga cikin su sun yi shahada tare da baffansu Imam Husaini (AS) a Karbala. [1] Bukhari da Muslim da Tirmizi, wajen ambatonImam Hasan(AS). [2] Ghazzali, cikin Ihya’u Ulum al-Din. [3] Don neman karin bayani kan wadannan nassosi da wasun su masu kama da su, ana iya komawa: Kashful-Gummah, juz’i na 2; al-Majalis al-Siniyyah da Tazkiratul-Khawas. Da wasun su masu yawa. [4] Taufik Abu Ilm, cikin Ahlul-bait, shafi na 264. [5] Nafakhat Min al-Sirah, talifin Mu’assar al-Balagh, shafi na 98. [6] Nafakhat Min al-Sirah, talifin Mu’assar al-Balagh, shafi na 100. [7] Inada aka ambataa sama, shafi na 98. [8] Inada aka ambataa sama. [9] Nafakhat Min al-Sirah, talifin Mu’assasar al-Balagh, shafi na 101. [10] Sheikh al-Dabrisi, cikin I’ilam al-Wara, shafi na 206; da Kashf al-Gummah fi Ma’arifatul-A’immah , juz’i na 2, shafi na 155. [11] Nafakhat Min al-Sirah, talifin Mu’assar al-Balagh, shafi na 105. [12] Ibin Abil-Hadid, cikin Sharh Nahjul-balagha, juz’i na 6, shafi na 38. * Zancen daukaka (Izza) ya saura tsaikon yunkurin Ahlulbaiti (AS). Imam Husaini ya yaki Umayyawa don Izza haka Imam Hasan ya yi sulhu da su don wannan. Manufar yunkurin wadannanImamai biyu na kore duk wani sabani a tsakaninsu. Manufarsu daya, hanyarsu daya kuma makiyansu daya. Zamunanu ne suka sassaba, wanda haka ya tilasta daukar matakin da ya daceda kowane yanayi. To ai Imam Husaini na nan a lokacin sulhun, kuma ya taimaka wajen ganin manufofin sulhun suntabbata. [13] Al-Karashi, cikin Hayat Imam Hassan , juz’i na 2, shafi na 281. [14] Al-Karashi, cikin Hayat Imam Hassan , juz’i na 2, shafi na 281 [15] Inda aka ambata a sama. [16] A’atham al-Kufi, a cikin, al-Futuh , juz’i na 4, shafi na 161. [17] Inda aka ambata a sama, shafi na 203. * Sai dai bayan Ja’adatu ta aiwatar da bukatar Mu’awuya, daga baya da ta nemi cika alkawari Mu’awiya bai cika mata ba. Ya kafa mata hujja da cewa: ‘Mai hankali ba ya auren wadda ta kashe mijinta’. Haka wannan ja’ira ta ga tabewa tun a duniya.
Posted on: Fri, 06 Sep 2013 21:45:55 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015