Taron juyayin wakiar Ashura na bana 1436 a kasar Saudi Arabia - TopicsExpress



          

Taron juyayin wakiar Ashura na bana 1436 a kasar Saudi Arabia cikin hotuna Kamar ko wacce shekara a bana ma a kasar Saudi Arabia an yi gagarumin taron juyayin wakiar Ashura a garuruwa da birane daban daban na kasar ciki harda Makka da Madina. Yan shiah mabiya Ahlul bait[AS] daga sassa daban daban na kasar suna ci gaba da raya ranakun wannan wata Na Muharram. A wasu bangarori na birnin madina duk inda ka duba ba abin da kake gani sai tutoci bakake da kyallaye bakake dauke da rubuce-rubucen nuna juyayi. Ga wasu hotuna da muka samu na juyayin ranar Ashura da aka gabatar a Qadeef a kasar Saudi Arabia.
Posted on: Mon, 10 Nov 2014 09:09:17 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015