Tattaunawa ce akayi tsakanin Uwargida da Maigida. Ga yarda - TopicsExpress



          

Tattaunawa ce akayi tsakanin Uwargida da Maigida. Ga yarda tattaunawar ta kasance : #Admin_Dinasir UWARGIDA : Mai gida a gaskiya nina gaji da zama cikin wannan bakin talaucin, yau akwai gobe babu. Don haka a san mai yiwuwa Eheee ! MAI GIDA : Uwargida ni ma fa talaucin nan ba son shi na ke ba, ya ishe ni, dole ce tasa nake hakuri, amma kwantar da hankalinki, na samo mafita. UWARGIDA : To inajin ka; yi sauri fadi mafitar nan kowace iri ce gara a yi ta, mudai fita daga talaucin nan don ni hakurina ya kare. MAI GIDA : Yawwa dama na ji liman ya ce Idan talauci ya yi ma mutum yawa to sai ya kara aure, sai ya samu dama-dama UWARGIDA : Aa mai gida, mu cigaba da zamammu cikin wannan halin, ya ma fi da wani arzikin ai gara talaucin. Malamai ma na cewa talauci alkhairi ne ! Mai gida ni yau ma azumi nake yi !
Posted on: Wed, 04 Dec 2013 20:07:52 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015