Via:- Tambaya Mabudin Ilmi Tambaya ta goma sha shida Q. MENENE - TopicsExpress



          

Via:- Tambaya Mabudin Ilmi Tambaya ta goma sha shida Q. MENENE FALALAR WATAN RAMADAN Ans. Azumin Ramadan yana da falaloli da ywa. Daga cikin falalar azumin sun hada da:- a. Yana kankare zunubin mutum kamar yadda yazo a hadisin Khuzaifah (R.A.) Manzon Allah {S.A.W} yace "fitinar mutum a cikin iyalansa, da dukiyarsa ko makwabcinsa sallah da azumi da sadaka suna kankaresu". (Bukhari). b. Yazo a hadisi, dukkan aikin Dan Adam nasane Malaiku suke rubuta shi, amma azumi wannan na Allah ne Shi Yake saka shi (hadisin ya tabbata a targhib wattarhib, juzI na farko shafi na 75). c. Hadisi kuma ya tabbata daga Jabir dan Abdullahi (R.A.) daga Manzon Allah {S.A.W.} cewar azumi garkuwane da dan Adam zaiyi garkuwa dashi daga wuta. sannan hadisi ya tabbata daga Muazu dan Jabal (R.A.) cewa hakika Manzon Allah {S.A.W.} yace dashi shin bazan nuna maka kofofin alheriba? Sai yace naam ya Rasulullah sai yace azumi garkuwane kuma akwai hadisin Abi Umamata (R.A.) yace, "Nace wa Manzon Allah ka umarceni da waani aiki da Allah Zai amfanar dani dashi sai yace ka lizimci azumi domin babu kamarsa" (dukkan wadanna hadisai sun tabbata a targhib, tahakikin Sheikh Albani juzuI na farko shafi na 578). d. Azumi kuma shine sababin tsoron Allah. e. A lokacin azumin Ramadan ana bude kofofin Aljanna, kuma ana kulle kofofin Jahannama sannan a daure shaidanu kamar yadda ya tabbata a hadisin Abi Huraira (Bukhari, 1899). f. Hadisi ya tabbata wanda Imam Tirmizi ya ruwaito cewar Manzon Allah {S.A.W.} yace "Bashin bakin mai azumi yafi kamshi fiye da turaren miski a wurin Allah" hadisine sahihi. Sannan wani hadisin ya tabbata daga Sahl bin Saad (R.A) daga Manzon Allah {S.A.W.) yace a cikin Aljanna akwai wata kofa ana kiranta Rayyanu, masu azumi zasu shigeta ranar tashin kiyama, babu wanda zai shigeta sai su. Idan sun shiga sai a kulleta babu wanda zai sake shiga (Bukhari 1896) Tirmizi ya kara bayani a cikin riwayarsa cewar wanda ya shigeta bazai ji kishin ruwaba har abada. Allah yasa mu dace.
Posted on: Fri, 19 Jul 2013 08:31:37 +0000

Trending Topics



tın
Memorial of Saint Catherine of Siena, Virgin and Doctor of the

Recently Viewed Topics




© 2015