Via Jibwis Nigeria JIBWIS TARON HADIN KAN KUNGIYOYIN AHLUSSUNNAH - TopicsExpress



          

Via Jibwis Nigeria JIBWIS TARON HADIN KAN KUNGIYOYIN AHLUSSUNNAH TA KASAR NIGERIA KARO NA FARKO, (COAN) MAI TAKEN (ZAMAN LAFIYA DA LUMANA DON CI GABAN KASA. Kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatis Sunnah ta kasa tana farin cikin gayyatar ‘yan uwa Musulmi Zuwa Wurin Taron Hadin kan Ahlusunnah ta kasar Nigeria karo na farko. Taron Ya gayyaci duk wani Musulmi Ahlussunnah daya fito daga ko wane lungu da sako daga cikin sassan gida Najeria ba tare da la’akari da Qabila ba. -Bako na Musamman: Shugaban Kasar Nigeria. -Babban Bako 1: Shugaban Kasar Jamhuriyar Niger. -Babban Bako 2: Mataimakin Shugaban Kasar Nigeria. -Guest Of Hounor: Hon. Aminu Waziri Tambuwal. (Speaker House of Representatives) -Chief Host: Governor Babatunde Raji Fashola (Executive Governor of Lagos State). -Speaker 1:Governor Ogbeni Rauf Aregbesola (Executive Governor of Osun State) -Grand Royal Father Of The Day: Alhaji Sa’ad Abubakar III (Sultan of Sokoto) -Conference Patron: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu (Former Governor of Lagos State) -Special Guest Father: Oba Ridwan Babatunde Osuolale Akiolu (The Oba of Lagos) -Chairman Of The Occation: Alh. Azeez Arisekola Alao (Are Muslim of Yoruba) -Speaker II- Professor Dawud Noibi, -Speaker III- Profesor Salisu Shehu. BAKI NA MUSAMMAN: -General Muhammadu Buhari RTD (Former Head of State) -General Ibrahim Badamasi Babangida RTD (Former Head Of State) -General Abdussalami Abubakar RTD (Former Head Of State) -Alh. Atiku Abubakar (Former Vice President). BAKIN TARO: Gwamnoni ashirin da uku daga dukkan sassan kasarnan. MASU TARO: Ash-Sheikh Imam Abdullahi Bala Lau (Chairman Jibwis Nigeria) Sheikh Dr. Ibrahim Jalo Jalingo (Chairman Council Of Ulama’u Jibwis Nigeria) Sheikh Muhammad Kabir Haruna Gombe (Secretary General Jibwis Nigeria) Eng. Mustapha Imam Sitti (National Director FAG of Jibwis Nigeria) Sheikh Dr. Alhassan Sa’eed Adam Jos (Board Of Trustee Jibwis Nigeria) Sheikh Yakubu Musa Hassan (Board Of Trustee Jibwis Nigeria) Sheikh Abubakar Giro Argungu (Chairman Working Committee Jibwis Nigeria) Za’a fara Wannan taro Ranar Asabar 15 February 2014. Da Misalin Karfe 10:00am na safe in Allah ya kaimu. A Dakin taro na tunawa da Prime Minister Marigayi Sir Abubakar Tafawa Balewa dake cikin garin Lagos (Tafawa Balewa Square, Lagos) Dandalin Jibwis Nigeria na Facebook mun gama shirin mu tsab dan kawo muku irin wainar da za’a toya da dumi dumin sa a wannan taro, Haka zalika kana iya kama Jibwis Radio duk inda kake a fadin duniyar nan dan sauraren abin da yake wakana a wannan taro mai albarka. Mahalarta taro ana so su isa Birnin Lagos tun ranar Jumu’a dan samun farkon taron da za’a fara a ranar asabar da safe. Muna Addu’an Allah ya bada ikon zuwa, ya kuma kiyaye dukkan fitina dake cikin tafiya yasa aje lafiya a dawo lafiya, ya kuma sa wannan taro ya zama sanadiyyar hadin kan dukkan Ahlussunnah a Nigeria, Amin. SANARWAN TA FITO NE DAGA OFISHIN SHUGABAN KUNGIYA TA KASA ASH-SHEIKH IMAM ABDULLAHI BALA LAU, TA HANNUN KAKAKIN SHUGABAN, USTAZ IBRAHIM BABA SULEIMAN.
Posted on: Mon, 10 Feb 2014 12:51:35 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015