Vincent Enyeama na sa ran Nigeria za ta zamo kasar Afrika da za ta - TopicsExpress



          

Vincent Enyeama na sa ran Nigeria za ta zamo kasar Afrika da za ta lashe gasar cin kofin duniya a karo na farko. Kyaftin din kwallon kafar Nigeria Vincent Enyeama ya ce ya yi imanin kasar za ta iya lashe gasar kofin duniya da zaa yi badi a Brazil. Super Eagles ce kungiyar Afrika ta farko da ta samu tikitin shiga gasar bayan ta doke Ethiopia 4-1 a wasanni biyu. Sai dai wannan yakini na Enyeama ya sabawa tarihi da kuma yanayin wasan Nigeria na baya bayan nan. Rabon Nigeria da cin wasa a gasar duniya tun nasarar da ta samu a kan Bulgaria a 1998 kuma ita ce karo na karshe da Super Eagles ta fito daga rukuninta. A tarihin gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya, kasashen Afrika uku ne kacal suka taba kai wa matakin daf da na kusa da na karshe: Cameroon a 1990, Senegal a 1992 da Ghana a 2010. Me za ku ce akan kalaman Enyeama? Admin→→→QPR™
Posted on: Mon, 18 Nov 2013 12:30:30 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015