WADANNENE RANAKUN FARKON ZUL HIJJA Ubangiji madaukakin sarki yana - TopicsExpress



          

WADANNENE RANAKUN FARKON ZUL HIJJA Ubangiji madaukakin sarki yana fada cikin alkur,ani mai girma cikin suratul fajar aya ta 1-3 ”INA RANSTUWA DA ALFIJIR, DA RANAKU GOMA, DA SHAF’,I DA WUTIRI”. Manyan malamai sunyi maganganu masu yawa akan wannan ayoyi, amma Abdullahi ibn Abbas Allah yakara yarda agareshi yace; “Abin da Allah yake nufi da Alfijir shine sallar Asubahi, Darare goma kuwa sune goman zulhijjah, shafa,i kuma shine halitta, Wutiri kuma shine Allah” Allah ya ambace su sune darare goma, domin ranaku ne Tara da dare goma, saboda girman da wadannan ranaku suke da shi har Allah{SWT}yayi ranstuwa dasu cikin littattafansa mai girma. DAUKAKA DA DARAJOJIN RANAKU GOMA NA ZULHIJJA Waddannan ranaku suna da matukar girma da daukaka domin an karbo Hadisi daga dan Abbas Allah ya kara yarda a gareshi, cewa shi ya ce “Acikin goman farko na zulhajji Allah ya karbi tuban Annabi Adam (A.S). Cikinsa ne Annabi Ibrahim ya gina Ka’aba, acikinsune Allah yayi munajati da Annabi Musa, har’ila yau acki aka saukarwa da Annabi Dawud gafara, aciki ranar Tarwiyya take, da ranar Arfat, da ranar layya, da kuma ranar Hajji. An karbo daga Abi Sa’id Alhudri (RTA) daga Manzon Allah (SAW) yace; “Sugaban watanni watan Ramadan, mafi girmansu kuma Zulhijja. FALALAR WATAN ZULHIJJA An karbo daga Jabir Allah ya kara yarda agareshi, daga Manzon Allah Salallahu Alaihi Wasallam yace; “Mafifitan Ranakun duniya Ranaku na Zuihijja…” Ankarbo daga Adda’u dan Rabi’a yace; ‘Naji Sayyada Aisha (RTA) tace; “Yakasance lokacin Annbi (SAW) wani mutum ya kasance idan watan Zulhijja ya kama sai ya wayigari yana Azumi sai wannan labari yariski Manzon Allah (SAW), Sai akazowa Annabi Alaihissalam da shi, ai yace dashi meyasa kake Azumtar wadannan ranaku?sai yace ya Ma’aikin Allah sun kasance ranakune na haduwa,kumaranakune na aikin hajji, sai nake so ubangiji ya hadani a cikin Addu’o’in da ake yi a ciki, sai Annabi Alaihissalam yaceda shi, ya tabbata ageka ko wacce rana da kai Azumikamar kayanta wuyaye dari ne,kayi hadaya da taguwa dai, kabayar da dawakai dari don daukaka Addinin Allah, amma kuma in ka Azumci ranar Arfa kamar ka yenta wuyaye dubu biyu ne, kayi hadaya da taguwa dubu biyu, kabaya da dawakai dubu biyu don Allah, kuma kamar ka Azumci shekarar da ta gabata ne da kuma shekara tagaba” Buhari da Muslim sn rawaito hadisi cewa Manzon Allah Alaihissalam yace; “Babu wasu wadansu ranaku da Allah Yafi son Alheri acikinsu fiye da wadannan ranaku, ina nufin ranakun fakon Zulhijja, sai akace ya ma’aikin Allah ko jihadi ne? sai yace ko da jihadi ne, sai dai mutumin day a fita kansa da dukiyarsa, sannan bai dawo da komai ba” FALALAR AZUMTAR RANAR ARFA Muslim ya rawaito cewa Manzon Allah Alaihissalam yace “Azmin ranar Arfa yana kankare zunuban shekaru biyu da suka gabata da shekara ta gaba.” An rawaito da sashin matan Manzon Allah cewa “Manzo Alaihissalam ya kasance yana azumtar tara na zulhijja” (Abu Dawud) Azumtar wadannan ranaku yana da matukar mahimmanci kamar yadda mukaji daga bakin shugaba Alaihissalam musamman ranar Tara ga Zulhijja wato ranar ARFA kamar yanda yazo a hadisin Buhari da muslim daya gabata. AIKATA AYYUKAN ALHERI Haka zalika anaso a yawaita sauran ayyukan alheri, domin Allah ya matukar son ayyukan alheri a ranakun, kamar yawaita tasbihi, da salatin Annabi, sada zumunci, yawaita nafil fili, da istigifari, da karatun Alkur’ani, kyautatawa iyali, ziyarar marasa lafiya, farantawa iyaye, da kara biyayya agaresu , tufatar da muminai da ciyar dasu ko shayar dasu, musamman masu tsananin bukata, jinkan marayu, musamman shafa kansu da kyautatamusu, da sauran ayyukan alhei, amma ubangiji yafi son a yawaita kabarbari a wadannan ranaku musamman a salloli goma sha biyar, daga sallar azahar taranar zuwa sallar asubahi ta ranar uku ga sallah, domin Abdullah Ibn Abbas ya kasance yana bin kasuwa yana kabarbari don tunawa mutane kada su shagala. SALLAR IDI BABBA Sallar idi Babba Sunnace mai karfi. Ubangiji Mai Girma da daukaka ya umarni da yinta cikin Littafinsa Mai Girma in da ya ke cewa: “Hakika mun baka Alkausara, kayi Sallah ga Ubangijinka, ka soke abin yankanka” (Suratul Kausar aya ta 1-2). Manzon Allah Alaihissalam ya yita kuma yayi umarni da yenta, ya fita don yin Sallar tare da Mata da Yara kanana, Sallar tana kara Imani da tsoron Allah. Ana yin tane a ranar Goma ga Zulhijja. LOKACIN SALLATARTA: Lokacin da ake Sallatar Idi babba shine daga lokacin da Rana ya dago, ana so ayita dawuri domin Mutane su samu suyi layya da wuri, kamar yadda Shugaba (SAW) ya aikata. LADABAN SALLAR IDI: Ladaban Salla sune kamar haka: 1. Wanka da sanya sababbin tufafi ko mafiya kyau, tare da fesa turare, saboda fadin Annabi Alaihissalam cewa: Manzon Allah ya umarcemu a ranakun idi biyu da musanya tufafi kyawawa, mu fesa turare mafi kamshi….,(Hakim) 2. Yana daga Ladaban ta kame baki har sai an dawo daga Masallaci, kamar yadda Aba Buharra yafada cewa: “Shugaba Alaihissalam ya kasance ba yacin Abinci ranar idi Babba har sai yadawo gida sai yaci daga layyarsa…” (Turmuzi) 3. Yin Kabarbari daga daren Idin har zuwa karshen ayyamul tashreek (wato kwanaki ukun bayan salla), lafazin Kabarbarin shi ne: ALLAHU AKBAR ALLAHU AKBAR LA’ILAHA ILLALLAHU ALLAHU AKBAR ALLAHU AKBAR WALILLAHIL HAMDU. Ana karfafa fadarsu yayin tafiya masallaci . 4. Yana daga Ladabanta canja hanyar da aka tafi yayin dawowa, Saboda Shugaba Alaihissalam ya kasance yana canja hanya a ranar idi (Buhari) 5. Yin Sallah a sarari ma’ana ba a cikin masallaci ba, sai dai idan da lalurar ruwa ko makamancin haka, to sai ayi a cikin masallaci. 6. Taya juna farin ciki tare da fadin musulmi ga dan’uwansa, Allah ya karba agareni ya karba a gareka. Kamar yadda aka rawaito Sahabban Manzo sun kasance idan sun hadu da yan’uwansu suna fadin Allah ya karba garemu da gareka (TAKABBALALLAHU MINNA WA MINKA). YANDA AKE YIN SALLAR IDI Yadda ake yin Sallar Idi shine, mutane su fito izuwa masallaci yayin da rana tafito, sai liman ya tsaya don Salla batare da kiran Salla ko ikama ba, zaiyi Raka’o’i biyu, a raka’ar farko zai yi kabarbari guda bakwai, tare da kabbarar harama, mutanen da suke bayansa za su rika yin kabbara a duk yayin da yayi kabbararsa, sai ya karanta Fatiha da Suratul A’ala, a bayyane. A raka’a ta biyu, zai yi kabarbari guda shida tare da kabbarar tsayuwa, zai karanta Fatiha da suratul Jashiyati ko suratul Shamsi, idan yayi sallama sai ya tashi don yiwa mutane huduba. Bayan ya budeta da yabo da Allah, da godiya a gareshi, sai ya kwadaitar da mutane akan falalar yin Layya da bayyanamusu hukumce-hukumcenta da yanda a ke yenta da kuma lokacin da ake yita, yayin daya kamala huduba sai mutane su taya junansu murna, sannan su koma zuwa gidajensu, ba za ayi sallar nafila ba bayan sallar Idi ko kafinta, sai dai in wanda sallar Idin ta kubuce masa ne, sai ya sallaceta raka’a hudu, saboda fadin Ibn Mas’ud Allah ya kara yarda a gareshi: “Wanda Sallar Idi ta kubuce masa ya sallaci raka’a hudu, amma wanda yariski wani abu tare da Liman koda zaman tahiya ne to sai ya tashi bayan liman yayi sallama ya sallaci raka’a biyu. Wadannan sune bayanai game da falalar da take cikin Goman Farko na Zulhijja tare da bayanai game da Sallar Idi babba, abin da aka karanta na daidai daga Allah ne Allah ya amfanar da masu karatu da shi, wanda akaji na kuskure daga gareni ne, Allah kada yabasu ikon yin amfani da kuskuren. Allah ya kara tsira da aminci ga shugaban halitta cikamakin Annabawa da ahalin gidansa, da sahabbansa da dukkan wadanda suka bishi da kyautatawa, A kulu kauli haza wa astagfirullaha li wa lakum, wassalamu alaikum warahamatullahi ta’ala wa barakatuhu.
Posted on: Sun, 06 Oct 2013 14:17:47 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015