WASANNI: Neymar Zai Yi Jinyar Makwanni Hudu Kungiyar kwallon - TopicsExpress



          

WASANNI: Neymar Zai Yi Jinyar Makwanni Hudu Kungiyar kwallon kafar Barcelona, ta tabbatar da cewa dan wasan gabanta, Neymar dan kasar Brazil zai shafe tsawon makwanni hudu yana jinyar raunin da ya samu a kafarsa a wasan da suka fafata da kungiyar Getafe a daren jiya a gasar Copa del Rey. Ana ganin zai yi wuya dan wasan ya samu damar buga wasan da Barcelona za ta kara da Manchester City ta Ingila a gasar UEFA Champions League a watan gobe.
Posted on: Fri, 17 Jan 2014 16:51:36 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015