WASIYYA ZUWAGA YAR UWA MUSULMA A RANAR AURENTA 1-KIJI TSORON - TopicsExpress



          

WASIYYA ZUWAGA YAR UWA MUSULMA A RANAR AURENTA 1-KIJI TSORON ALLAH A ZAMANTAKEWARKU Allah zai sanya miki mafita akan dukkan al‘amuranki! 2-AURE IBADANE Ki sani cewa Aure ibada ne, za ki iya Gani da jin abubuwan da rai ba ya so,don haka kiyi Hakuri sai ki samu Aljannarki cikin sauki. 3- HAKURI & JURIYA Rayuwar aure ba na wata 1 ko shekara 1 ko 50 bane, rayuwa ce ta har a bada sai da HAKURI kuma da JURIYA. 4-MIJI SHUGABANE AGAREKI Don haka duk abin da yake bukata a kowani lokaci dole ki aikatashi muddin ba sabon Allah bane. 5- NESANTAR ABUN MIJI YAKE KI Dukkan abun ki Maana abunda Mijinki baya so ki nisance shi, domin yawan sabawa miji zai janyo miki tsana. 6- YIN ABUNDA MIJI YAKE SO Ki kula da dukkan abin mijin ki yake so, ki aikata shi ko da za ki wahala a aikatawa, domin wannan shine zai sa mijinki ya kara kaunarki,Kuma Ki sani Aljannarki tana karkashin duga-dugan mijinki, Maana da yin biyayya agareshi zaki shiga Aljannah. 7-RIKE SIRRI Kada ki yarda wani ya san sirrin da ke tsaninki da mijinki ko da kuwa Yan uwankine. 8- YIN TAKA TSANTSAN DA SHAWARWARIN KAWAYE ki kula da dukkan shawarar da kowace ‘kawa za ta ba ki,ki zabi mace me Ilimi da Addini a matsayin a bokiyar shawara. 9-KYAUTATA ZAMANTAKEWA DA YAN UWAN MIJI Kiyi Iya kokarin da zaki iya wajen kyautata zamantakewarki da yan uwan Mijinki (Iyayensa,yayyu nsa,kannensa da sauran danginsa) 10- GASKIYA DA RIKON AMANA Ki yiwa zamantakewarku Ado da yin gaskiya, duk abunda zakiyi kiyi gaskiya kuma ki rike amanar mijinki. Wadanda Basuyi Aureba Allah Ya Basu Ikonyi Wadanda Sukayi Allah Ya Basu Zaman Lafiya. kushiga nan kuyi #like din shafinmu na koyarwa akan addinin musulunci... Rayuwar Musulunci Rayuwar Musulunci Rayuwar Musulunci Rayuwar Musulunci
Posted on: Thu, 07 Nov 2013 10:56:55 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015