WAYYO CIWON HAUKA, ALLAH KA RABA MU DA CIWON HAUKA Wani Likita - TopicsExpress



          

WAYYO CIWON HAUKA, ALLAH KA RABA MU DA CIWON HAUKA Wani Likita ne na mahaukata (pshychist) a gidan mahaukata (pshychatery), bayan tsawon lokaci da ya dauka yana basu horo domin ganin ya taimaka musu sun fita daga halin da suke ciki, domin ya ware wadanda suka dan samu nutsuwa daga cikin su, sai watarana ya tara su wuri guda, ya dauko Alli (Chalk) a aljihunsa sai ya zana hoton kofa (Door) a jikin bangon gidan, ya koma gefe yace dasu duk wanda yabi waccan kofar har gida zata kai shi, nan da nan mahaukata suka fara karo da juna suna dukan bango suna faduwa wasu ma harda suma. Can sai ya gano wani shi kadai yana zaune, sai yace dashi ya akai ana tafiya gida na ganka anan a zaune, sai kuwa mahaukacin nan yace dashi ai zuba musu ido nayi su gama haukansu su gama mukullin yana gurina Me zaku ce dangane da wannan aiki na masu hankali
Posted on: Mon, 11 Nov 2013 23:47:22 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015