WAYYO YA ZANYI DA RAINA Daga:- Sadiiyah Sulaiman Slm Admin dan - TopicsExpress



          

WAYYO YA ZANYI DA RAINA Daga:- Sadiiyah Sulaiman Slm Admin dan Allah kuyi post din labarina, wlh na shiga tsaka mai wuya maza sun cuceni, sun gama da rayuwana, yanzu ni duk na tsani soyayya wlh. Na dade ina haduwa da maza kala-kala tun ina yarinya nake soyayyah, amma akwai wasu samarina da suka yaudareni na farko mun dade muna tare dashi lokaci daya ya juya min baya, dama ba sona yake ba yaudara ce kawai, nayi kuka sosai lokacin daya gujeni har rashin lafiya nayi, haka na 2 ma, to tun daga lokacin nayi bankwan da soyayyah bada son raina ba, dan a rayuwa ina son soyayyah burina kullum naga masoyina yazo yana furtamin kalaman soyayyah ji nake kamar na tashi sama saboda dadi, amma a haka dole na dena kula kowa saboda karna kara fadawa tarkon maza. To abun daya tayar min da hankali, yanzu wani guy ya takura min kullum saimin naci yake na rasa yadda zanyi wlh, gashi guy din ya kusa sace min zuciya saboda dadadan kaman shi wayyo fans ya zanyi. Ku taimaka min.
Posted on: Sun, 01 Sep 2013 07:54:41 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015