Wanda ya fi kowa kudi a China Wang Jianlin zai gina masana’antar - TopicsExpress



          

Wanda ya fi kowa kudi a China Wang Jianlin zai gina masana’antar shirya fina-finai a China a kan Naira Tiriliyan 1 da biliyan 296. Za a gina wannan masana’antar ne a kingdao da ke Yamma maso Gabashin China daga Yunin 2016 zuwan Yunin 2017. Mai kudin ya bayyana hakan ne a lokacin wani biki da kamfaninsa na Dalian Wanda Group ya shirya kan bunkasa sana’ar fim a China Lahadin da ta gabata. Za a gina dakin shirya fina-finai 20 da dandamali mai fadi da tsawon kafa dubu dari da takwas wanda zai zama dandamali mafi girma a duniya. Za a kuma gina cibiyar bincike da bunkasa harkar fim da sinimomi da gidan ajiya na ‘yan wasan fim da sauransu. Za a kuma gina wurin shakatawa da hotel guda 8 don masu yawon bude idanu. Jaruman da suka halarci bikin sun hada da Nicole Kidman da Ewan McGregor da Catherine Zeta-Jones da John Trabolta da kuma Leonardo DiCaprio, daga China kuma akwai Zhang Ziyi da Jet Li da Tony Leung da sauransu. Kamfanin ya ce ya yi yarjejeniyar farko da kamfanonin kasashen waje da hukumomin kasashen waje da kuma gidajen talabijin na kasashen waje da suke shirya fina-finai don su shirya fina-finai 30 cikin wannan shekarar. Sai dai kamfanin ya ki sanar da wadanne hukumomi da kamfanoni da kuma gidajen talabijin ne. Wang ya ce: “Ina fata za mu jawo hankalin kamfanoni da suke shirya fina-finai na kasar China fiye da 50, don a shirya fina-finai 100 a dakin shirya fina-finan da za mu gina a nan (China) wanda hakan zai jawo hankalin masu shirya fina-finai daga Nahiyar Turai da Gabas ta Tsakiya da sauransu.”
Posted on: Thu, 03 Oct 2013 13:33:51 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015