Wani Bagwari ne ya je kasuwa yana aikin dako, sai rigima - TopicsExpress



          

Wani Bagwari ne ya je kasuwa yana aikin dako, sai rigima ta kaure; ’yan sandan kwantar da tarzoma suka zo kasuwar suna tambayar mutane daya bayan daya. Suna cewa: “Kai wane ne, mene ne aikinka.” Kowa yana amsa tambayoyin daidai yadda ake bukata. Sai tambaya ta zo kan dangwari, aka tambaye shi mece ce sana’arsa. Maimakon ya amsa da cewa yana sana’ar dako ne, sai ya ce: “Mu muna daukar kayan mutane ne.” Nan take ’yan sandan suka kama shi, suka saka shi motarsu.
Posted on: Wed, 04 Dec 2013 20:31:43 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015