Wani Bazazzage ne yaje Amurka, sai ya hadu da wani dan Jarida, Sai - TopicsExpress



          

Wani Bazazzage ne yaje Amurka, sai ya hadu da wani dan Jarida, Sai dan Jaridar ya tambaye shi. Dan Jarida: Waye Shugaban Kasar Najeriya? Bazazzage: JEGA Dan Jarida: Ba Chairman din Zabe na kasa nake nufi ba, Shugaban Kasa. Bazazzage: Na gayama sunan sa JEGA. Dan Jarida: Da alama baka da masaniya kan Shugaban kasar ku, ko kuma kana da tabin kai. Bazazzage: (Cikin fushi) hala tsohon ka ne mai tabin kai da toshewar basira, wanda ka kasa fahimtar abu a takaice. Dan Jarida: ( ya danja da baya, a tinaninsa Bazazzage ya tabu) na yarda JEGA ne Shugaban kasarku. Bazazzage: (yayi murmushi) nasan har yanzu baka gane ba. JEGA sunan Shugaban kasarmu ne a takaice. J= Jonathan E= Ebele G= Goodluck A= Azzalimi. Dan Jarida: kai Allah yayi dan Najeriya da fasahar iya zance!!!
Posted on: Tue, 12 Nov 2013 19:57:44 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015